Coronavirus: Wani bidiyo ya nuna yadda wasu mata suka ba hammata iska a kan tsummar takarda

Coronavirus: Wani bidiyo ya nuna yadda wasu mata suka ba hammata iska a kan tsummar takarda

- Cutar coronavirus na yada tsoro a zukatan mutane a fadin duniya sannan ana ta daukar matakan hana kwasar cutar sosai

- An gano bisiyon yadda wasu mata uku yan kasar Australia suka ba hammata iska a kan tsimmar takarda

- Hakan na zuwa ne a lokacin da mazauna Aussie suka siye dukkanin tsimmar takardar, inda kantuna suka rage babu komai

Cutar Covid-19 ya jefa duniya cikin hali na rudani. Inda mutane sama da 102,000 suka kamu da cutar sannan yawan mutane da ke mutuwa suna karuwa, hakan ya sanya mutane a fadin duniya suna kokarin kare kawunansu da iyalansu.

A kasar Australia, al’umma na ta siye tsummar takarda don shirin koda t abaci sannan haka na haddasa rashin jituwa.

An gano wasu mata uku a cikin bidiyo suna ba hammata iska kan pakitin tsummar takarda. Bidiyon ya yi fice a shafukan sadarwa sannan hakan ya nuna yadda mutane suka tsorata da cutar coronavirus.

Daya daga cikin matar ta kasance da kwandon siyayya cike da tsummokaran takarda sannan ita kuma dayar matar na son pakiti dayane kawai.

Hakan ya haddasa rigima sannan a cewar jaridar The Guardian, yan sandan Australia sun tuhumi matan a kan fadan.

KU KARANTA KUMA: Yanzun-nan: An tabbatar da mutum na biyu da ke dauke da coronavirus a Najeriya

Kalli bidiyon a kasa:

A wani labarin kuma, mun ji cewa cikin matakan da take dauke wajen takaita yaduwar cutar Coronavirus, Kasar Saudiyya ta bada umurnin kulle dukkan makarantu da jami'o'in masarautar fari daga ranar Litinin har ila ma sha'a llahu.

Kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya SPA ta sanar da cewa ma'aikatar Ilimin kasar ta sanar da hakan ne a ranar Lahadi, 8 ga watan Febrairu 2020.

Jawabin yace: "An yanke shawarar kulle dukkan makarantu ne saboda kyakkyawar soyayyar da shugabancin ke yiwa yaranta kan tsaronsu kuma za'a samar da wasu hanyoyin ilmantar da su daga gidajensu."

Ministan harkokin ilimin Saudiyya ya bada umurnin ilmantar da yara daga gidajensu ta hanyar na'urorin zamani. Kawo yanzu, mutane 11 sun kamu da cutar a kasar ta Saudiyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel