Lamine Yamal Ya Tsokano Fushin Isra'ila da Ya Ɗaga Tutar Falasdinu a Barcelona
- Kasar Isra’ila ta yi martani mai zafi bayan ɗan wasan Barcelona ya daga tutar Falasdinu yayin murnar lashe gasar Laliga
- Abin da tauraron kulob din Barcelona ya yi ya jawo maganganunm yayin da wasu yabonsa duk da suka da ya ke sha
- Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce matakin dan wasan ya tayar da kiyayya, yayin da ake ci gaba da rikicin Gaza tsakanin Isra’ila da Hamas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel - Dan wasan Barcelona mai shekara 18, Lamine Yamal, ya jawo ce-ce-ku-ce a duniya yayin faretin murnar lashe gasar Laliga.
Lamarin ya tayar da kura ne bayan daga tutar Falasdinu a lokacin murnar lashe da aka gudanar a birnin Barcelona.

Source: Facebook
Falasdinu: Isra'ila ta caccaki Lamine Yamal

Kara karanta wannan
Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi martani kan 'ganawa' da Netanyahu ana tsaka da yakin Iran
Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya soki matakin dan wasan a shafin X inda ya ce hakan ya tayar da kiyayya ga Isra’ila.
Yamal ya daga babbar tutar ne daga cikin motar bas da suke kai yayin zagayen murnar da kungiyar ta yi tare da magoya baya a ranar Litinin 11 ga watan Mayun shekarar 2026.
Rahotanni sun nuna cewa kusan mutane 750,000 suka halarci bikin murnar nasarar Barcelona wacce ta lashe gasar Laliga a karo na 29.
Ya ce:
“Lamine Yamal ya zabi tayar da kiyayya kan Isra’ila yayin da sojojinmu ke yaki da kungiyar ta’addanci ta Hamas, kungiyar da ta kashe mutane, ta ci zarafi tare da kona yara Yahudawa, mata da tsofaffi a ranar 7 ga Oktoba, 2023.”
Har ila yau, ya bukaci kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da ta barranta kanta da abin da ɗan wasanta ya yi tare bayyana cewa ba ta tare da irin wannan kiyayya da goyon bayan ta'addanci.

Source: Getty Images
Wallafar da Yamal ya yi ta jawo maganganu
Bayan haka, Yamal wanda Musulmi ne ya wallafa hotunansa dauke da tutar Falasdinu a shafinsa na Instagram domin nuna goyon baya duk da cewa ya goge daga baya.

Kara karanta wannan
Majalisar dinkin duniya ta sa baki kan harin sojojin sama da ya kashe farar hula a Zamfara
Kasashen duniya da dama da kuma jama’a a Spain sun ci gaba da sukar yakin Isra’ila a Gaza saboda yawan mutanen da suka mutu.
Hakan ya sa ake yawan ganin nuna adawa a wasanni da sauran harkokin nishadi kan yakin wanda a baya ba kasafai ake ganin irin haka ba.
An kuma samu irin wannan ce-ce-ku-ce a gasar tseren keke ta Spanish Vuelta da kuma Eurovision, inda wasu kasashe suka kaurace wa gasar saboda halartar Isra’ila.
Ana sa ran Yamal zai wakilci Spain a gasar cin kofin duniya ta 2026 da za a yi a Amurka a watan Yunin wannan shekara da ake ciki.
Isra'ila ta hukunta sojanta kan cin mutuncin Yesu
A baya, kun ji cewa a kwanakin baya sojojin Isra'ila sun janyo cece-kuce bayan wulakanta mutum mutumi na mamar Yesu Almasihu a Kudancin Lebanon.
Bayan yaduwar hotunan wulakancin da sojojin suka yi, rundunar sojojin Isra'ila ta ve ta kaddamar ta bincike kan lamarin.
Rundunar sojojin ta bayyana cewa ta yankewa sojojin da ke da hannu a aika-aikar zama a gidan yari sakamakon laifin da suka yi.
Asali: Legit.ng