Yanzun-nan: An tabbatar da mutum na biyu da ke dauke da coronavirus a Najeriya

Yanzun-nan: An tabbatar da mutum na biyu da ke dauke da coronavirus a Najeriya

- An tabbatar da mutum na biyu da ke dauke da coronavirus a Najeriya

- Ministan lafiya, Osagie Ehanire, ya sanar da hakan ta hannun hukumar kula da yaduwar cututtuka na Najeriya (NCDC)

- Mutum na biyu da ke dauke da cutar ya kasance cikin wadanda aka killace sakamakon hulda da dan kasar Italiya da ya shigo da cutar Najeriya

Ministan lafiya, Osagie Ehanire, ya sanar da samun wani mutum na biyu da ke dauke da cutar coronavirus a Najeriya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa mutumin ya yi hulda da dan kasar Italiya da ya shigo da cutar coronavirus Najeriya.

Yanzun-nan: An tabbatar da mutum na biyu da ke dauke da coronavirus a Najeriya
Yanzun-nan: An tabbatar da mutum na biyu da ke dauke da coronavirus a Najeriya
Asali: Twitter

An tattaro cewa mutumin ya kasance daya daga cikin wadanda aka killace.

Cibiyar kula da yaduwar cututtuka na Najeriya (NCDC) ce ta tabbatar da hakan a wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Litinin, 9 ga watan Maris.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama masu asiri 3 da kan mutum a Lagas

"An gano mai dauke da cutar ne a jihar Ogun cikin mutanen da aka kebance tun tuni, kuma an gano cutar a jikinsa ne a kokarin da muke na gano duk wadanda suka yi alaka da mai dauke da cutar na farko dan kasar italiya."

A wani lamari makamancin haka mun ji cewa cikin matakan da take dauke wajen takaita yaduwar cutar Coronavirus, Kasar Saudiyya ta bada umurnin kulle dukkan makarantu da jami'o'in masarautar fari daga ranar Litinin har ila ma sha'a llahu.

Kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya SPA ta sanar da cewa ma'aikatar Ilimin kasar ta sanar da hakan ne a ranar Lahadi, 8 ga watan Febrairu 2020.

Jawabin yace: "An yanke shawarar kulle dukkan makarantu ne saboda kyakkyawar soyayyar da shugabancin ke yiwa yaranta kan tsaronsu kuma za'a samar da wasu hanyoyin ilmantar da su daga gidajensu."

Ministan harkokin ilimin Saudiyya ya bada umurnin ilmantar da yara daga gidajensu ta hanyar na'urorin zamani. Kawo yanzu, mutane 11 sun kamu da cutar a kasar ta Saudiyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

iiq_pixel