Yanzu Yanzu: Gwamnatin Lagas ta tabbatar da samun karin mutane 3 da ake zargin suna dauke da coronavirus

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Lagas ta tabbatar da samun karin mutane 3 da ake zargin suna dauke da coronavirus

- Kwamishinan lafiya a jahar Lagas, Frafesa Akin Abayomi, ya bayyana cewa a yanzu haka akwai lamarin da ake zargin cutar coronavirus ne guda uku a jahar

- Abayomi ya ce an gano wasu mutane uku da ake ganin suna dauke da cutar

- Kwamishinan na jahar Lagas ya bayyana cewa an yiwa marasa lafiyan gwaji sannan an killace su a Yaba Lagas

Kwamishinan Lafiya a jahar Legas Farfesa Akin Abayomi ya tabbatar da killace wasu mutum uku da ake zargi sun kamu da cura Coronavirus.

Kwamishinan na jahar Lagas ya bayyana cewa an yiwa marasa lafiyan gwaji sannan an killace su a Yaba da ke jahar a matsayin matakin hana yaduwar cutar.

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Lagas ta tabbatar da samun karin mutane 3 da ke dauke da coronavirus
Yanzu Yanzu: Gwamnatin Lagas ta tabbatar da samun karin mutane 3 da ke dauke da coronavirus
Asali: UGC

Nan gaba ake sa ran za a saki sakamakon gwajin da aka yi wa mutanen.

Farfesa Akin Abayomi ya ce daya daga cikin mutanen uku dan Najeriya ne da ya dawo kasar ranar Litinin bayan shafe mako daya a Faransa.

Daga baya kuma ya nuna alamun ciwon kai da matsalar numfashi. Sauran mutanen kuma matafiya ne daga Ingila da kuma China.

KU KARANTA KUMA: Bana shirin karban mulki daga hannun Buhari - Fayemi

A baya mun ji cewa Kwamishinan Lafiya na Jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi ya ce an killace wani ɗan Najeriya da ya dawo daga kasar Faransa a Cibiyar Kula da Cututtuka masu Yaɗuwa da ke Yaba, Legas.

A yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a ranar Laraba, Abayomi ya ce wata an turo mutumin ne zuwa cibiyar daga wani asibitin kuɗi a Legas.

Kwamishinan ya ce zai sanar da sakamakon gwajin da aka yi wa mutumin da zarar an kammala.

Abayomi ya ce, "Ɗan Najeriya ne da ya tafi kasar Faransa, ya yi kwanaki bakwai a Faransa sannan ya dawo Legas kwanaki uku da suka gabata kuma yana fama da ciwon kai da matsalar numfashi.

"An killace shi yanzu, ana yi masa gwaje-gwaje a halin yanzu, ina jiran sakamakon gwajin," in ji Abayomi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel