Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Tsige sarkin Kano, Muhammadu Sanusi da Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta yi a ranar Litinin, 9 ga watan Maris, ya nuna karara cewa iyakar matsayin sarakunan gargajiya a karnin damokradiyya.
Fadar Shugaban kasa ta yi martani ga lamarin tsige Muhammadu Sanusi II daga matsayin Sarkin Kano da gwamnatin jahar ta yi, inda ta bayyana cewa gwamnoni masu ci na iya amfani da karfin mulki kan masarautun da ke a karkashinsu.
Tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar, wanda shine shugaban wani kwamitin yin sulhun a tsakanin tsohon Sarki Muhammadu Sanusi da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano ya tofa nasa kan tsige Sarkin.
Tsohon sarkin na Kano, ya nuna godiya ga Allah a kan wannan kaddara da ta same shi, sannan ya yi kira ga al’umma das u zauna lafiya sannan su yi wa sabon sarki biyayya.
Al'umman Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakunansu a kan matakin da gwamnatin jahar Kano ta dauka na tsige sarki Muhammadu Sanusi na II.
A yau Litinin, 9 ga watan Maris ne gwamnatin jahar Kano karkashin jagorancin, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta tsige Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II.
Kamar yadda kuka sani an jahar Kano ta tsinci kanta a cikin wani yanayi a yau Litinin, 9 ga watan Maris, inda aka tsige sarkin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II.
Rahotanni da muke samu a yanzu ya nuna cewa jami’an tsaro sun kama Sarki Sanusi sannan sun tafi da shi. Sai dai zuwa yanzu babu wani cikakken bayani a kan inda aka nufa da shi ko kuma halin da ya ke ciki.
Sarkin Borgu, mai martaba, Alh (DR) Muhammed S. Haliru Dantoro a ranar Asabar, 7 ga watan Maris ya amince dakatar da wasu manyan masarautar bayan wani taron gaggawa da aka gudanar a fadar Gbemusu.
Aisha Musa
Samu kari