Ainahin abin da ya sa ake dauke sarakuna daga garinsu bayan cire su

Ainahin abin da ya sa ake dauke sarakuna daga garinsu bayan cire su

Tun bayan da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tsige Muhammadu Sanusi na II daga kujerar sarauta tare da kuma mayar da shi jahar Nasarawa a matsayin sabon wajen da zai ci gaba da rayuwarsa, 'yan Najeriya da dama suka dasa ayar tambaya kan dokar da ta ce a dinga yi wa sarakuna irin wannan daurin talalar.

Wani masanin tarihi a Kano Malam Ado Kurawa ya bayyana cewa a shekarar 1930 ne Turawan mulkin mallaka suka fara kirkirar dokar da ta ce duk wani sarki da aka sauke daga mulki ko aka ci shi a yaki ko ya sauka don radin kansa, to za a dauke shi daga garin da yake zuwa wani matsuguni daban da zai samu mafaka, shafin BBC Hausa ta ruwaito.

Dokar ta ce sarkin ba shi da izinin zabar wajen da zai zauna sai inda aka zabar masa, sannan ba zai sake shiga garin da ya mulka din ba har bayan rai.

Ainahin abin da ya sa ake dauke sarakuna daga garinsu bayan cire su

Ainahin abin da ya sa ake dauke sarakuna daga garinsu bayan cire su
Source: UGC

Masanin tarihin ya ce: "Sun kirkiri wannan doka ce don gudun yin sarakuna biyu a gari daya, wato tsoho da sabon sarki, da kuma gudun samun sabanin ra'ayi.

"Sannan suna jin tsoron kar a samu matsala a harkokin mulki ta yadda bangarori biyu na tsohon sarki da sabon sarki za su dinga adawa da juna ko nuna karfin iko."

Masana shari'a da dama na cewa ya kamata zuwa yanzu a daina amfani da duk wata doka ta Turawan Mulkin mallaka idan dai har ba ta cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ko su lauyoyin Sarki Sanusi sun ce al'adar dauke sarakunan da aka sauke zuwa wani waje daban ba ta cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Sashe na hudu, karkashin sashe na 41 a dokar 'Yancin walwala na kundin tsarin ya bayyana cewa: ''Kowane dan Najeriya yana da damar zama a duk inda yake so a fadin kasar, kuma babu wani dan kasar da za a kora daga cikinta ko a hana shi dawowa bayan ya fita daga cikinta.''

Lauyoyin Sunusin sun ma sun kara kafa hujja da cewa "Mun yi matukar mamaki da har yanzu ake gudanar da irin wannan al'ada a Najeriyar yau, musamman ga shugabannin siyasa.

KU KARANTA KUMA: Sau 3 gwamnatin Kwankwaso na aike wa Sanusi da takardar gargadi - Gwamnatin Kano

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Atoni Janar na jahar Kano, Ibrahim Muktar ya ce gwamnatin jahar ba ta kori tsigaggen Sarki, Muhammadu Sanusi na II daga jahar ba.

Muktar ya ce gwamnatin jahar ta yi jawabi dalla-dalla a sanarwar da ta saki a ranar Litinin cewa an tsige Sanusi amma babu inda ta nuni ga an kore shi.

Atoni Janar na Kanon ya fadi hakan ne a wani shirin Channels TV Sunrise Daily a ranar Laraba, 11 ga watan Maris.

Muktar ya ce jami’an tsaro sun yanke shawarar tserewa da Sanusi daga jahar Kano sakamakon rahotanni kwararru da suka samu.

Ba sabon abu bane fitar da tsigaggen sarki daga gari domin wanzar da zaman lafiya a jahar, inda ya kara da cewa wannan bai saba kundin tsarin mulki wacce ta bayar da yancin yawo ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel