Yanzun-nan: Tsohon Sarkin Kano Sanusi ya yi jawabi mai taba zuciya bayan tsige shi daga kujerarsa

Yanzun-nan: Tsohon Sarkin Kano Sanusi ya yi jawabi mai taba zuciya bayan tsige shi daga kujerarsa

Tsigaggen sarkin Kano, Muhammadu Sanusi, ya yi furucinsa na farko bayan tsige shi daga kan kujerar sarauta.

Tsohon sarkin na Kano, ya nuna godiya ga Allah a kan wannan kaddara da ta same shi, sannan ya yi kira ga al’umma das u zauna lafiya sannan su yi wa sabon sarki biyayya.

Ya ce:“A kullun muna cikin godiya ga Allah S.W.T, a cikin ni’imominsa wadanda basa karewa, a cikin ni’imomin da Allah ya yi mun, Allah S.W.T ya kaddara an nada ni sarki ranar 8 ga watan Yuni, 2014, ya raya ni cikin rayuwa da lafiya.

Shekara kusan shida a kan wannan gado na wannan gaado namu mai albarka. A yau Ubangiji S.W.T wana ya bani sarautar ya kaddara, ya karba. Koda yaushe muna fada cewa sarauta ajali ne da ita, kwanakin da Allah ya rubuta a kan gado kayadaddu ne, idan ranakun nan sun zo ko ana so ko ba a so sai an tafi, saboda haka mu mun karbi dukkanin abunda Allah ya yi.

"Mun yarda, mun gode, mun yi farin ciki kuma mun san shine alkhairi a gare mu. Muna gode ma al’umman Kano a dukkanin shekarun nan irin kauna da suka nuna mana da soyayya da biyayya da addu’o’i. Muna gode ma dukkanin wadanda suka taimaka mana a cikin harkar mulki, yan majalisarmu da hakimai da suka bamu goyon baya. Muna gode ma yan uwa na zumunci wadanda suka tsaya, suka kare martabarmu da martabar gidan nan.

"Muna kira ga al’umma a zauna lafiya, wanda Allah ya ba wa sarauta mun umurci iyalanmu, da ‘yaýanmu, da wadanda muke da iko a kansu da duk wanda Allah ya ba wa, al’umma suka yi masa muba’ia su je su yi masa muba’ia. Su bi shi, su kare martabarsa."

Kalli bidiyon a kasa:

KU KARANTA KUMA: Tuna baya: Hotunan sarakuna 7 da aka taba tube wa rawani

A baya un ji cewa tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi II mai murabus ya tattara inasa inasa ya koma kauyen Loko dake cikin karamar hukumar Nassarawa ta jahar Nassarawa.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito tsohon Sarkin ya samu rakiyar hadimansa da wasu jami’an gwamnatin jahar Kano inda suka sauka a filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikwe da yammacin Litinin, 9 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel