Dalilai 5 da suka sa Ganduje ya sauke Sarki Muhammadu Sanusi II

Dalilai 5 da suka sa Ganduje ya sauke Sarki Muhammadu Sanusi II

Kamar yadda kuka sani an jahar Kano ta tsinci kanta a cikin wani yanayi a yau Litinin, 9 ga watan Maris, inda aka tsige sarkin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II.

Sai dai sakataren gwamnatin jahar, Alhaji Usman Alhaji ya fitar da wata sanarwa kan dalilin tsige sarkin.

Dalilai 5 da suka sa Ganduje ya sauke Sarki Muhammadu Sanusi II
Dalilai 5 da suka sa Ganduje ya sauke Sarki Muhammadu Sanusi II
Asali: Instagram

Ya ce daukaci majalisar dokokin jahar sun yarda a cire Sanusi.

Ga wasu dalilai biyar da ake ganin sune suka sa aka tsige Sarki Sanusi:

1. Cewa Sarki Sanusi ya nuna halin rashin biyayya ga wasu umurni da Gwamnan jahar Abdullahi Umar Ganduje ya bayar, wadanda suka hada da rashin halartan taruka da gwamnati ke gayyatarsa ba tare da dalili ba. A cewar sanarwar idan har aka bar shi ya ci gaba da haka zai bata mutuncin masarautar.

2. Bisa ga dalili na biyu shine cewa an tsige Sarki Sanusi be don kare mutunci, al’adda, addini da kuma kimar masarautar wacce aka kafa shekaru dubbai da suka gabata.

3. Dalili na uku da ake ganin ya haddasa tsigewar nasa shine cewa yawan sukar da Sarkin ke yiwa gwamnatin Ganduje.

Irin haka ne ya sa tun farko aka fara samun sabani tsakaninsa da gwamnati harma aka yi yunkurin sauke shi da kuma bincikar yadda aka kashe kudin masarautar ba bisa ka’ida ba.

4. Abu na hudu shine yadda magoya bayan Ganduje suka zargi sarkin da tsoma baki a harkar siyasa harma da zarginsa da goyon bayan dan takarar PDP a zaben gwamnan 2019 da aka yi a jahar.

Koda dai Sanusi ya karyata hakan, lamarin ya kawo baraka a tsakaninsa da Ganduje.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Jami'an tsaro sun kama Sarki Sanusi

5. Dama tun bayan da Ganduje ya kacaccala masarautar Kano zuwa yanka biyar mutane suka fara zargin za a tsige Sanusi.

Lamarin ya yi matukar tunzura masarautar Kano da Sarki Sanusi.

A wani labarin kuma, mun ji cewa biyo bayan tsige tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi II mai murabus, diyarsa ta fito a kafar sadarwar zamani ta Twitter tana yin gargadi tare da kashedi ga masu jajanta musu, inji rahoton TheCables.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito diyar Malam Sunusi mai murabus, Yusrah Sunusi ta yi kira ga abokan huldarta a kafar sadarwar zamani ta Twitter da cewa su daina jajanta musu saboda ba mutuwa aka musu ba, kuma basu mutu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng