Sarkin Borgu ya dakatar da manyan yan fada kan taimaka wa makiyaya

Sarkin Borgu ya dakatar da manyan yan fada kan taimaka wa makiyaya

- Sarkin Borgu ya dakatar da kimanin manyan masarautar biyar a jahar Niger

- Mai martaban ya dakatar da manyan kansilolin ne sakamakon rahotannin cewa suna taimaka wa makiyaya

- Dakatarwar nasu ya fara aiki nan take bayan wani taron gaggawa da aka gudanar a masarautar

- Wadanda lamarin ya shaa sune Wazirin Borgu, Ubandoman Borgu, Madakin Borgu, Garkuwan Borgu da Sadaukin Borgu

Sarkin Borgu, mai martaba, Alh (DR) Muhammed S. Haliru Dantoro a ranar Asabar, 7 ga watan Maris ya amince dakatar da wasu manyan masarautar bayan wani taron gaggawa da aka gudanar a fadar Gbemusu.

A cewar PR Nigeria, an dakatar da manyan masarautar kimanin su biyar biyo bayan zargin tallafa wa makiyaya shiga masarautar sabanin umurnin Sarkin da Gwamnatin jahar Niger.

Sarkin Borgu ya dakatar da manyan yan fada kan taimaka wa makiyaya

Sarkin Borgu ya dakatar da manyan yan fada kan taimaka wa makiyaya
Source: Depositphotos

Basaraken a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren masarautar Borgu, Abubakar Jubriel ya sanar da dakatar da Wazirin Borgu, Ubandoman Borgu, Madakin Borgu, Garkuwan Borgu da Sadaukin Borgu.

KU KARANTA KUMA: Jami'an tsaro sun mamaye fadar sarkin Kano

A wani labarin kuma, mun ji cewa Mambobin majalisar dokokin jihar Kano sun barke da fada da safen nan yayinda kwamitin binciken sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, ke shirin gabatar da rahoton kwance masa rawani.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa rikicin ya fara ne yayinda mataimakin kakakin majalisar, Hamisu Chidari, ya nemi izinin gabatar da rahoton yau.

Amma yan majalisar jam'iyyar adawa ta PDP suka ce a dakatad da gabatar da rahoton binciken sai ranar Talata domin kara dubi cikin rahoton; kawai sai rikici ya barke wanda ya kai ga dan majalisa mai wakiltar Warawa ya dauke sandar majalisa.

Har ila yau mun ji cewa cewa gwamnatin jihar Kano ta tsige mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu.

Hadimin gwamnan Kanon kan sabbin kafafen yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 9 ga watan Maris, 2020.

Yace: "Majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da tsige sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel