Yadda Harin Sojojin Sama Ya Kashe Farar Hula da 'Yan Ta'adda a Zamfara
- Ana ci gaba da magana kan harin sojojin saman Najeriya wanda ake zargin ya hallaka fararen hula da dama a jihar Zamfara
- Majiyoyi daga yankin sun ba da tabbacin cewa kasuwar da aka kai harin, wuri ne wanda yake hada farar hula da 'yan ta'adda
- Sun bayyana cewa mafi yawan kauyukan da ke Arewacin Zurmi suna rayuwa ne a karkashin ikon 'yan ta'adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Wani harin sojojin sama da aka kai a jihar Zamfara ya haddasa rasuwar fararen hula da 'yan ta'adda.
Mazauna yankin sun bayyana cewa harin wanda rundunar sojojin sama ta Najeriya ta kai ranar Lahadi, 10 ga watan Mayun 2026 a wata kasuwar dabbobi a ƙauyen Tunfa da ke Zurmi, jihar Zamfara, ya kashe ’yan ta’adda da farar hula da dama.

Source: Facebook
Jaridar Premium Times ta kawo rahoton cewa mazauna yankin ne suka sanar mata da cewa harin ya shafi farar hula da 'yan ta'adda.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta yi zargin cewa aƙalla farar hula 100 ne suka mutu a lamarin, sai dai dakarun soji sun musanta wannan ikirarin.
Harin sojoji sama ya hallaka mutane
Sai dai wasu mazauna yankin biyu da jaridar ta tattauna da su sun bayyana cewa babu wanda ya iya tantance adadin waɗanda aka kashe ko suka ji rauni yayin harin saman, amma sun haɗa da ’yan ta’adda da kuma farar hula mazauna yankin.
Tumfa wani kauye ne mai dogaro da noma da ke kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar, kuma kasuwarsa tana samun halartar mutane daga maƙwabciyar ƙasar, da kuma jihohin Zamfara da Katsina, musamman daga Shinkafi da Jibiya.
Ranar Lahadi da misalin ƙarfe 12:37 na rana, mazauna yankin sun ce wani jirgin yaƙin sojoji ya shawagi a sararin samaniyar ƙauyen na wasu mintuna kafin ya saki bama-bamai a kasuwar da ke wajen garin.

Kara karanta wannan
Sojoji sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'adda, an kashe manyan kwamandojin Boko Haram a Borno
Duk da shaidun asarar rayukan farar hula, gwamnatin jihar Zamfara da hedikwatar tsaro ta kasa sun dage kan cewa ’yan ta’adda ne kawai bama-baman suka kashe.
Farar hula sun rasa rayukansu a Zamfara
Wani mazaunin kauyen Mashema, Dalhatu Musa, ya bayyana cewa:
“Mutum uku da na sani sun rasa rayukansu, yayin da wasu biyu suka ji rauni. Dukkansu daga kauyenmu suke."
Malam Dalhatu Musa, wanda manomi ne, ya ce yakan halarci kasuwar Tumfa kafin matsalar tsaro ta ta’azzara.
Ya bayyana sunayen mutum ukun da suka mutu a matsayin Sa’idu Sulaiman, Lawali Hanazuwa, da Maryam Anaruwa, inda ya bayyana su a matsayin ’yan uwa a gare shi. Ya ce Maryam matashiya ce mai sayar da dafaffen abinci a kasuwar.
“Alhaji Mola da Ibrahim Amadu su ne abokai na biyu da suka ji rauni. Alhaji Mola yana asibitin FMC da ke Gusau saboda raunukansa sun yi tsanani."
- Malam Dalhatu Musa
'Yan ta'adda na da iko a yankunan Zamfara
Lokacin da aka tambaye shi ko ’yan ta’adda ne ke gudanar da kasuwar ko kuma suna halartar kasuwar dabbobin, Malam Musa ya ce yawancin yankunan Arewacin Zurmi suna ƙarƙashin ikon ’yan ta’adda ne.

Kara karanta wannan
Sojojin sama sun hallaka jagororin 'yan ta'adda a Zamfara bayan yi masu ruwan wuta
“’Yan ta’addan ma suna zuwa kasuwar; wannan wani abu ne da kowa ya sani. Amma mazauna gari da dama ma suna zuwa can don saya da sayarwa domin ba mu da wani zaɓin, tunda gwamnati ta gaza magance matsalar tsaro."
Suna shiga cikin garuruwanmu suna gudanar da kasuwanci, tunda ba mu da bindigogi ko ikon yaƙarsu, me kuke so mu yi?”
- Malam Dalhatu Musa
Mazauna yankin da aka tattauna da su sun ce an kai farar hular da suka ji rauni zuwa cibiyar lafiya ta matakin farko da ke Mashema, babban asibitin Zurmi, babban asibitin Shinkafi, da kuma babban asibitin Tarayya (FMC) da ke Gusau.
Wani shugaban al'umma daga kauyen Kware wanda ya tsere zuwa Shinkafi ya bayyana cewa:
“Yaya gwamna zai ce waɗanda aka kashe duka ’yan bindiga ne? Abin ya shafi mutanenmu daga Kware da suka tafi kasuwar. An tura wasu daga cikinsu zuwa FMC Gusau saboda suna da munanan raunuka.”

Source: Original
Akwai 'yan ta'adda a kasuwar
Wani ma’aikacin ƙungiyar likitoci ta MSF a Zurmi, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa mutane da dama da abin ya shafa suna Babban Asibitin Zurmi. Amma ya ƙi bayar da adadin waɗanda aka kwantar ya zuwa yanzu.
Wani mazaunin garin Zurmi, Aliyu Alhaji-Muntari ya bayyana cewa:
"Gaskiya ne, akwai ’yan ta'adda da yawa a kasuwar ranar. Dole ne sojojin su kasance sun ga ’yan ta'addan da bindigoginsu, amma akwai farar hula da dama a wurin, kuma ya kamata sojojin su sani cewa wannan kasuwa ce ta farar hula.”
Majalisar dinkin duniya ta bukaci a yi bincike
A wani labarin kuma, kun ji cewa Majalisar dinkin duniya ta nuna damuwarta kan harin da sojojin sama suka kai a jihar Zamfara.
Shugaban kwamitin kare hakkin dan Adam na Majalisar dinkin duniya, Volker Turk, ya bukaci a gaggauta gudanar da bincike.
Volker Turk ya bayyana cewa bai kamata fararen hula da kayayyakinsu su kasance wuraren da za a rika farmaka ba.
Asali: Legit.ng

