Bayan Tatile Yaransa a Tantancewar APC, Fubara Ya Magantu kan Alakarsa da Ita
- Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya yi karin haske game da jita-jitarda ake yadawa wai yana shirin barin APC
- Fubara ya bayyana cewa gwamnatinsa ta mayar da asibitin masu tabin hankali na Rumuigbo zuwa babban asibiti domin inganta lafiyarsu
- Gwamnan ya ce aikin asibitin ya nuna kudirin gwamnatinsa wajen aiwatar da ayyukan da ke taba rayuwar jama’a kai tsaye tare da inganta walwalar mutanen Rivers
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sake yin magana game da yada jita-jita kan zamansa a APC.
Fubara ya tabbatar da cewa har yanzu yana nan daram a jam’iyyar APC duk da rade-radin da ake yadawa.

Source: Twitter
Fubara ya bayyana hakan ne bayan duba aikin sake gina asibitin masu tabin hankali da aka mayar zuwa babban asibiti a yankin Rumuigbo da ke Obio/Akpor, cewar Channels TV.
Yadda ake yada barin Sim Fubara APC
Ya ce rahotanni da fassarori da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa ya sauya jam’iyya ba gaskiya ba ne ko kadan.
A cewarsa, wasu mutane na amfani da bayanai daga shafukan sada zumunta wajen gabatar da shi ta hanyar da ba ta dace ba.
Gwamnan ya jaddada cewa bai bar APC ba, kuma har yanzu yana nan a matsayin cikakken dan jam’iyyar mai mulki a Najeriya.
Wannan raɗe-raɗin na zuwa ne yayin da APC ta ki tantance masu nemam takara daga Rivers fiye da 60 daga cikin 98 a Abuja.
Da yake magana kan aikin asibitin, Fubara ya ce gwamnati ta gano akwai karancin cibiyoyin lafiya a yankin lokacin wata ziyarar aiki da ta gabata.
Ya bayyana cewa asibitin koyarwa na jami’ar Port Harcourt ne kadai babban wajen jinya mafi kusa ga mazauna yankunan da abin ya shafa.
Saboda haka, gwamnati ta ga dacewar samar da babban asibiti domin kula da lafiyar mutanen Rumuigbo da sauran yankunan da ke makwabtaka da su.

Source: Original
Rivers: Fubara ya fadi alkawuran da ya cika
Fubara ya nuna gamsuwa da kammala aikin, yana mai cewa hakan na daga cikin alkawuran da gwamnatinsa ta cika wa jama’ar jihar Rivers.
Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da fifita ayyukan da za su inganta rayuwa da walwalar al’ummar jihar kai tsaye, cewar Punch.
Fubara ya kuma sha alwashi kan ci gaba da ayyukan alheri da samar da abubuwan ci gaba da za su inganta rayuwar mazauna jihar.
An cire mutanen Fubara a tantancewar APC
Mun ba ku labarin cewa wasu daga cikin magoya bayan gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara sun fuskanci matsala yayin da jam'iyyar APC ke tantance masu neman takara a zaben 2027 da ake tunkara.
An tabbatar da cewa kwamitin ya kifar da manyan na hannnun daman gwamna Fubara da suka halarci wajen tantance masu son tsayawa takara.
A daya bangaren kuma, yawancin mutanen da ke biyayya ga Ministan Abuja, Nyesom Wike da ya yi takun saka da Fubara sun tsallake tantancewar.
Asali: Legit.ng

