EFCC Ta Cafke Shugaban Babbar Hukuma a Gwamnatin Tinubu kan Badakalar N500bn
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta cafke shugaban wata hukuma a gwamnatin Mai girma Bola Ahmed Tinubu
- Jam'ian hukumar EFCC sun cafke shugaban hukumar makamashi ta Najeriya, Mustapha Abdullahi kan zargin halasta kudaden haram
- Majiyoyi daga hukumar EFCC sun bayyana cewa zargin da ake yi wa shugaban na hukumar makamashi ta Najeriya ya shafi kudade wanda adadinsu ya kai N500bn
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, sun cafke shugaban hukumar makamashi ta Najeriya (ECN), Mustapha Abdullahi.
Jami'an na hukumar EFCC sun cafke Mustapha Abdullahi ne kan zargin aikata laifuffukan halasta kuɗaɗen haram.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce wata majiya a cikin hukumar yaki da cin hanci da rashawa, wadda ta nemi a sakaye sunanta saboda ba a ba ta izinin yin magana kan lamarin ba, ta tabbatar da kamun a ranar Laraba, 13 ga watan Mayun 2026.
Meyasa EFCC ta cafke Mustapha Abdullahi?
Majiyar ta bayyana cewa an kama Mustapha Abdullahi ne a Abuja kuma yana tsare a hannun hukumar EFCC.
A cewar majiyar, zargin da ake yi masa ya shafi kuɗaɗe da aka kimanta sun kai Naira biliyan 500.
“Mun kama shugaban hukumar makamashi ta Najeriya, Dr Mustapha Abdullahi, kan laifuffukan halasta kuɗaɗen haram. An kama shi kuma a halin yanzu yana tsare a hannunmu. Kuɗin sun kai kimanin Naira biliyan 500."
- Wata majiya
Ƙoƙarin samun tabbaci daga mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya ci tura domin ba a same shi ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoton.
Yaushe aka nada shi shugabancin ECN?
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Mustapha Abdullahi a matsayin shugaban hukumar makamashi ta Najeriya ne a ranar 24 ga Oktoba, 2023.
An naɗa Mustapha Abdullahi ne a matsayin shugaban ECN bayan ya shafe shekaru fiye da 10 yana aiki a hukumar NUPRC ta Najeriya.

Kara karanta wannan
Hukumar JAMB ta fitar da mafi karancin makin shiga jami'a na shekarar 2026 a Najeriya
An shigar da korafi kan Mustapha Abdullahi
Jaridar The Cable ta ce a watan Disamba na shekarar 2025, wata ƙungiyar farar hula mai suna NACAT, ta shigar da koke ga Tinubu, EFCC da ICPC, kan zargin cin hanci da rashawa a cikin hukumar ECN.

Source: Twitter
Ƙungiyar ta zargi shugaban na ECN da shiga cikin abin da ta siffanta da "tsari na yaudara da aka tsara shi sosai" wanda ya shafi ba da kwangilolin fitulun titi na hasken rana ba bisa ƙa'ida ba tare da biyan kuɗaɗe da suka kai ɗaruruwan miliyoyin naira ga kamfanoni biyar waɗanda ake zargin mutane guda ne suka mallaka kuma suke tafiyar da su.
Ta yi zargin cewa dukkan kamfanonin biyar an yi musu rajista ne a cikin mako guda tsakanin ƙarshen watan Oktoba zuwa farkon watan Nuwamba na shekarar 2023, sannan suna amfani da adireshi guda a Abuja, kuma ana zargin daraktocinsu guda ne.
EFCC na neman tsohuwar Minista
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar EFCC ta ayyana Sadiya Umar Farouq a matsayin wadda take nema ruwa a jallo.
Hukumar EFCC ta ayyana neman tsohuwar Ministar harkoki jin kai da rage talaucin ne ruwa a jallo bisa zargin amfani da ofis ba daidai ba da karkatar da kuɗin gwamnati da suka kai biliyoyin Naira.
Tsohuwar ministar ta yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari daga shekarar 2019 zuwa 2023.
Asali: Legit.ng

