Cif Audu Ogbe ya zama Shugaban kungiyar dattawan arewa

Cif Audu Ogbe ya zama Shugaban kungiyar dattawan arewa

Tsohon ministan noma, Cif Audu Ogbe ya zama Shugaban kungiyar dattawan arewa wato ACF, sannan tsohon karamin ministan wuta da karafuna, Alhaji Murtala Aliyu ya zama babban sakataren kungiyar.

Shugabannin kwamitin zabar shugabannin Laftanal Janar MI Wushishi da Malam Bukar Zarma ne suka saki sunayen sabbin shugabannin a ranar Talata, 10 ga watan Maris a Kaduna.

Har ila yau an zabi Ambasada Dr. Shehu Malami, Sanata Fred Oti da Ambasada Ibrahim Mai Sule a matsayin Shugabannin kwamitin amintattu.

Cif Audu Ogbe ya zama Shugaban kungiyar dattawan arewa
Cif Audu Ogbe ya zama Shugaban kungiyar dattawan arewa
Asali: Depositphotos

Sauran wadanda aka ba mukamai sune; Sanata Ibrahim Ida (Mataimakin shugaba), Sanata Salihu Matori (Mataimakin shugaba) Alhaji Tambari Ahmed (Mataimakin babban sakatare) Alhaji Yakubu Gobir (Hadimin babban sakatare ) Mista Emmanuel Yaweh sakataren labarai, Ambassador Ayuba Ngbako mataimakin sakataren labarai da Kanal Aliyu Audu a matsayin hadimin sakataren labarai.

Sauran yan kwamitin masu ruwa da tsaki sune; Alhaji Shuaibu Shehu , Alhaji Yahaya Abdullahi, Alhaji Mohammed, Alhaji Babasule Bisalla, Ms Fati E. Ibrahim, Alhaji Yusuf Jega, Alhaji Ibrahim Moriki, Chief Kevin Kwapn, Alhaji Ajiya Idris, Hajia Saadatu Abdullahi, Alhaji Hassan Yusufu, da kuma Alhaji Mohammed Yakubu.

KU KARANTA KUMA: Mafakar Sanusi: Gwamnan Nasarawa ya kira taron gaggawa na manyan sarakuna

A wani labari na daban, mun ji cewa babban malamin addinin Islama da ke zaune garin Kaduna, Sheikh Ahmed Gumi, ya bayyana cewa tsarin sarautar gargajiya ya gama lalacewa, a saboda haka bashi da wani sauran tasiri a Najeriya.

Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne yayin da ya ke tofa albarkacin bakinsa a kan tube rawanin Sanusi II da gwamnatin jihar Kano ta yi a ranar Litinin, 9 ga watan Fabrairu.

A ranar Litinin ne gwamnatin Kano, ta bakin Usman Alhaji, sakataren gwamnatin jiha, ta sanar da sauke Sanusi II daga kujerar sarkin Kano bisa zarginsa da rashin biyayya ga sabbin dokokin masarautun jihar Kano da aka kirkira a karshen shekarar 2019.

A martaninsa a kan sauke Sanusi, wanda ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta, Sheikh Gumi ya bayyana cewa, "tsarin sarautar gargajiya abu ne mai kima da daraja a duniyar da, amma yanzu, abin takaici, bashi da wani tasiri saboda addini da kuma nada wadanda basu cancanta ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel