Da dumi-dumi: Jami'an tsaro sun kama Sarki Sanusi

Da dumi-dumi: Jami'an tsaro sun kama Sarki Sanusi

Rahotanni da muke samu a yanzu sun kawo cewa a ranar Litinin, 9 ga watan Maris, jami’an tsaro sun kama tsigaggen Sarkin Kano sannan suka dauke shi daga birnin mai tsohon tarihi bayan tsaurara matakan tsaro.

An tattaro cewa jami’an tsaron sun yi jahar Nasarawa da shi inda zai kare rayuwarsa a mafakar.

Kafin a dauke shi, an rufe Sanusi a masarautar inda jami’an tsaro na DSS, yan sanda da sojoji suka hana shiga da kuma fita.

An kama shi ne bayan jami’an tsaro sun rufe fadar.

Da dumi-dumi: Jami'an tsaro sun kama Sarki Sanusi
Da dumi-dumi: Jami'an tsaro sun kama Sarki Sanusi
Asali: Twitter

Wata majiya daga gidan gwamnati ta bayyana cewa Gwamna Abdullahi Ganduje, wanda ya jagoranci taron gaggawa na masu ruwa da tsaki zai sanar da sabon sarki a kowani lokaci.

A safiyar yau Litinin, 9 ga watan Maris ne dai majalisar dokokin jahar ta Kano ta amince da sauke Sanusi daga kujerar sarauta.

Idan zamu tuna, Legit.ng ta ruwaito cewa Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa gwamnatin jihar Kano ta tsige mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu.

Hadimin gwamnan Kanon kan sabbin kafafen yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 9 ga watan Maris, 2020.

Yace: "Majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da tsige sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II."

KU KARANTA KUMA: Iyayi: Ku daina mana ta’aziyya, ba mutuwa aka mana ba – diyar Malam Muhammadu Sunusi II

Hakazalika, sakataren gwamnatin jihar, Usman Alhaji, ya saki jawabi kan dalilin da yasa gwamnatin jihar ta tunbuke sarkin Kano daga kujerarsa.

Ya ce an kwancewa Sanusi Lamido Sanusi rawani ne saboda yan zubar da mutunci da kuma ko oho da dokokin masarautar.

Baya ga haka, Usman Alhaji ya ce Sarkin ya daina halartan dukkan ganawa da gwamnatin jihar ta shirya ba tare da wani uzuri kwakkwara ba kuma hakan rashin biyayya ne ga gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel