Hukumar JAMB Ta Fitar da Mafi Karancin Makin Shiga Jami'a na Shekarar 2026 a Najeriya

Hukumar JAMB Ta Fitar da Mafi Karancin Makin Shiga Jami'a na Shekarar 2026 a Najeriya

  • Hukumar JAMB ta kayyade maki 150 a matsayin mafi karanci ga wadanda ke neman gurbin shiga jami'o'i a shekerar 2026 a Najeriya
  • An cimma wannan matsaya ne a taron tsara manufofin ba da guraben shiga manyan maiaratu, wanda ya gudana a Abuja yau Litinin
  • Taron ya samu halartar Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, tare da shugabannin jami’o’i, kwalejojin fasaha da na ilimi da sauran masu ruwa da tsaki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) ta fitar da mafi karancin makin da ake bukata kafin bai wa dalibi gurbi a jami'o'in Najeriya.

Hukumar JAMB ta amince da maki 150 a matsayin mafi karancin makin da dalibai za su samu domin samun gurbin shiga jami’o’i a fadin Najeriya a shekarar karatu ta 2026.

Kara karanta wannan

SDP 2027: Jam'iyyar adawa ta farko ta tsaida ɗan takarar shugaban kasa

Jamb.
Dalibai na tsakiyar zana jarabawar shiga manyam makarantu da hukumar JAMB ke shirya wa a Najeriya Hoto: JAMB
Source: Twitter

JAMB ta kayyade makin shiga jami'a

A rahoton Tribune Nigeria, JAMB ta sanar da hakan ne a taron tsara manufofin shiga makarantu da aka gudanar a Abuja ranar Litinin.

Hukumar ta kuma bayyana maki 150 a matsayin mafi karancin makin shiga kwalejojin jinya, yayin da na kwalejojin fasaha ya kasance maki 100 cikin maki 400 na jarabawar UTME.

Taron ya samu halartar Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, tare da shugabannin jami’o’i, kwalejojin fasaha da na ilimi da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren ilimin manyan makarantu.

Dalilin kayyade mafi karancin maki

Sabon tsarin na nufin cewa duk dalibin da ke neman shiga jami’ar Najeriya a shekarar 2026 dole ne ya samu akalla maki 150 a jarabawar UTME kafin a yi la’akari da shi.

JAMB ta ce maki da aka kayyade, wanda ake kira National Minimum Tolerable UTME Scores, yana nufin babu wata makarantar gaba da sakandare da za ta iya bai wa dalibi gurbin karatu idan bai kai wadannan maki ba.

Kara karanta wannan

2027: Mata 6 da suka nuna sha'awar takarar gwamna a Najeriya

Sai dai makarantu na da damar saka maki fiye da wanda aka kayyade ga masu neman shiga, kamar yadda tashar Channels tv ta kawo.

A bara ma an kayyade maki 150 domin shiga jami’o’i, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan Najeriya, inda wasu suka bayyana cewa makin ya yi kasa sosai.

Minista ya yi maganar karancin shekaru

Da yake jawabi a taron, Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya ce gwamnati na nan a kan bakarta na shekaru 16 a matsayin mafi karancin shekarun shiga manyan makarantu.

“Mun yi hakan ne domin samar da daidaito tsakanin bai wa kowa dama da kuma tabbatar da cewa dalibai sun shirya ta fuskar ilimi," in ji shi.
Tunji Alausa.
Ministan ilimi na Najeriya, Dr. Tunji Alausa yana tsakiyar aiki a ofishinsa a Abuja Hoto: @DrTunjiAlausa
Source: Facebook

Alausa ya kara da cewa ko da akwai yara masu hazaka ta musamman, dole ne a kula da irin wadannan lokuta cikin tsauraran ka’idoji domin kare martabar tsarin ilimi.

Dalilan da suka jawo faduwar JAMB 2025

A wani rahoton, mun kawo muku manyan dalilai uku da ake hasashen su ne suka jawo faduwar da dalibai suka yi a jarabawar JAMB ta bara.

Kara karanta wannan

2027: Nafiu Bala ya sake birkita ADC bayan fara sayar da fom din takara

Sakamakon jarabawar da hukumar JAMB ta fitar a shekarar 2025 ya nuna cewa 75% na daliban da suka rubuta jarabawa sun samu maki kasa da 200.

Hakan ya nuna cewa wannan ne karo na uku aka samu faɗuwa jarabawar UTME mafi muni a Najeriya tun 2016.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262