Ba mu kori Sanusi daga Kano ba – Gwamnatin Ganduje
Atoni Janar na jahar Kano, Ibrahim Muktar ya ce gwamnatin jahar ba ta kori tsigaggen Sarki, Muhammadu Sanusi na II daga jahar ba.
Muktar ya ce gwamnatin jahar ta yi jawabi dalla-dalla a sanarwar da ta saki a ranar Litinin cewa an tsige Sanusi amma babu inda ta nuni ga an kore shi.
Atoni Janar na Kanon ya fadi hakan ne a wani shirin Channels TV Sunrise Daily a ranar Laraba, 11 ga watan Maris.

Asali: Depositphotos
Ya ce: “Idan kun saurari sakataren gwamnatin jahar lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai kan lamarin tsige sarkin daga kujerarsa, babu inda ya ambaci cewa an kori sarkin daga jahar Kano.
“Don haka hukuncin gwamnati a lokacin da aka tsige sarkin a ranar Litinin shine cewa a cire shi daga kan kujerar sannan an nada sabon sarki. Batun korarsa baya daga cikin shawarar gwamnatin jahar Kano.
“Muna ta ji a kafofin watsa labarai cewa an kore shi amma abun da na sani shine cewa an fitar dashi daga jahar Kano amma ba wai korarsa na daga cikin hukuncinmu ba. Babu wani abu makamancin haka a iya sanina."
Muktar ya ce jami’an tsaro sun yanke shawarar tserewa da Sanusi daga jahar Kano sakamakon rahotanni kwararru da suka samu.
Ba sabon abu bane fitar da tsigaggen sarki daga gari domin wanzar da zaman lafiya a jahar, inda ya kara da cewa wannan bai saba kundin tsarin mulki wacce ta bayar da yancin yawo ba.
KU KARANTA KUMA: Buhari ne ya bayar da umarnin tumbuke Sarkin Kano – Kwankwaso
A baya mun ji cewa gwamnatin jahar Kano a ranar Talata, 10 ga watan Maris ta bayar da karin dalilai da suka sanya ta tsige Muhammad Sanusi daga matsayin Sarkin Kano.
Ta ce sau uku gwamnatin tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso na aike wa Sanusi takardar gargadi kan rashin mutunta al’ada.
Kakakin gwamnan Kano, Mista Salihu Yakasai ya yi magana ne a wata tashar radiyo mai zaman kanta ta Rave FM a Osogbo.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng