Mafakar Sanusi: Gwamnan Nasarawa ya kira taron gaggawa na manyan sarakuna

Mafakar Sanusi: Gwamnan Nasarawa ya kira taron gaggawa na manyan sarakuna

Gwamna Abdullahi Sule na jahar Nasarawa ya kira taron gaggawa na manyan sarakuna a jahar.

Wata majiya ta bayyana cewa Gwamnan ya kira taron ne domin duba yadda za a magance lamarin muhalli da al’amuran tsigagen sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

An mayar da tsohon sarkin Kanon Jahar Nasarawa domin ci gaba da rayuwarsa.

Sarakunan da ake sanya ran za su halarci taron sun hada da sarkin Lafia, Justis Sidi Dauda Bage (mai ritaya) da Sarkin Keffi, Alhaji Shehu Chindo Yamusa III.

Gwamna Abdullahi Sule ya fito ne daga gidan sarauta domin mahaifinsa, Alhaji Sule Bawa, ya kasance mai mukami na uku a Gudi, wani tashar jirgin kasa a karamar hukumar Akwanga.

Mafakar Sanusi: Gwamnan Nasarawa ya kira taron gaggawa na manyan sarakuna
Abdullahi Sule
Asali: Twitter

An tsara Sanusi II zai zauna a garin Loko na karamar hukumar jahar Nasarawa a jahar Nasarawa.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa da farko an tsara dauko sarkin daga Kano zuwa garin Opanda a karamar hukumar Toto ne amma sai aka canja shawara a farat daya.

DUBA WANNAN: Tsige Sanusi: 'Ba ni na kar zomon ba'; Fatima Ganduje ta yi wa masu sukarta martani

Manyan yan Najeriya irin su sarkin Lafia, Justis Sidi Bage sun gana da Gwamna Abdullahi Sule Sannan suka nemi a sauya masa wuri. Sauran mutanen da suka kira Gwamnan sune Alhaji Aliko Dangote da Janar Aliyu Gusau da sauransu,” in ji majiyar.

An tattaro cewa Gwamna Sule ya amince a kai tsohon sarkin Loko inda ya fi wurin farko na farkon.

Fulani ne ke zama a garin Loko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel