Duniya Labari: Mahajjaciya daga Najeriya Ta Riga Mu Gidan Gaskiya a Saudiyya
- An yi rashi na daya daga cikin Alhazan Najeriya da suka isa kasa mai tsarki watau Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2026
- Wata mahajjaciya da ta fito daga jihar Nasarawa ta yi bankwana da duniya tana da shekara 70 a birnin Makka na kasar Saudiyya
- Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Nasarawa ta bayyana cewa marigayiyar ta yi korafin rashin lafiya, sai dai duk da kokarin da likitoci suka yi, ba su samu damar ceto ranta ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Makka, Saudiyya - Wata mahajjaciya 'yar Najeriya daga jihar Nasarawa, Hajiya Rukayya Halliru, ta rasu a birni mai tsarki na Makka da ke kasar Saudiyya.
Hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Nasarawa ta tabbatar da rasuwar marigayiyar a ranar Laraba, 13 ga watan Mayun 2026.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa shugaban hukumar, Mallam Idris Ahmad Almakura, ya bayyana faruwar lamarin ga manema labarai a Makka.
Mahajjaciya daga Nasarawa ta rasu a Makka
Ya ce marigayiya Hajiya Rukayya Haliru, wadda ta fito daga ƙaramar hukumar Keffi, tana da shekaru 70 a duniya.
A cewar jami’in, ta yi kukan rashin lafiya ne, kuma duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi, ta yi bankwana da duniya a safiyar yau.
Shugaban hukumar tare da sauran jami’ai da ’yan uwan marigayiyar, sun halarci asibitin domin kula da shirye-shirye da jigilar gawarta zuwa Masallacin Harami da ke Makka don gudanar da sallar jana’iza.
An ba mahajjata shawara kan kula da lafiya
Ya kuma shawarci sauran Alhazai da su rika kula da lafiyarsu yadda ya kamata kuma su kai rahoton duk wata alama ta rashin lafiya cikin gaggawa ga likitocin da ke aiki tare da hukumar, jaridar Tribune ta kawo labarin.
Mallam Idris Ahmed Almakura ya miƙa ta’aziyyar hukumar ga gwamnatin jihar Nasarawa, iyalan marigayiya Hajiya Rukayya Halliru, da daukacin ma’aikata da shugabannin hukumar jin daɗin Alhazai.
A wata tattaunawa, Abdulwab Aboki, ɗaya daga cikin dangin marigayiyar wanda ya shaida yadda aka gudanar da komai, ya nuna godiyar iyalinsu ga hukumar saboda goyon baya da gaskiyar da ta nuna a tsawon wannan mawuyacin lokaci.

Source: Twitter
Karanta wasu labaran kan mahajjatan Najeriya
- Hajjin bana: Maniyyaciya daga Taraba ta rasu awanni kadan kafin tafiya Saudiyya
- Hajjin bana: Wata maniyyaciya daga Najeriya ta rasu 'yan awanni da isa Saudiyya
- Dan damfara ya sace wa mahajjaciya 'yar Najeriya daloli a Madina
Barayi sun yi wa maniyyata sata a Saudiyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani mahajjaci dattijo Bafullatani wanda ya fito daga jihar Jigawa ya bayyana cewa an yi masa fashin makudan kudi a birnin Makkah na kasar Saudiyya.
Dattijon mai suna Baba Katanga daga kauyen Katanga da ke karamar hukumar Kiyawa ya ce ya rasa dala 400 bayan hawa tasi daga Masallacin Harami zuwa otel dinsa.
Hakzalika, wani mahajjaci Bafullatani daga karamar hukumar Jahun shi ma ya rasa dukkan dalolinsa bayan da ake zargin wani direban tasi ya sace masa su.
Asali: Legit.ng

