Bidiyon tuna baya: Sarkin Kano jami’in gwamnati ne, muna iya tsige shi – Marigayi Rimi

Bidiyon tuna baya: Sarkin Kano jami’in gwamnati ne, muna iya tsige shi – Marigayi Rimi

Tsige sarkin Kano, Muhammadu Sanusi da Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta yi a ranar Litinin, 9 ga watan Maris, ya nuna karara cewa iyakar matsayin sarakunan gargajiya a karnin damokradiyya.

An kawo cewa basaraken baya mutunta umurni daga ofishin gwamnatin jahar da sauran hukumomin doka.

Sai daitun bayan tsige Sanusi da gwamnatin Kano ta sanar ake ta wasu tambayoyi kan makomar sarakunan gargajiya a tsakanin siyasa.

Ana ta sukar matakin Ganduje, amma wannan ba shine karo na farko da zababben gwamna ke yi wa

Kafin shi, Marigayi tsohon Gwamnan jahar Kano, Abubakar Rimi a 1982, ya furta cewa Sarki jami’in gwamnati ne, wanda ake biya da kudin gwamnati, sanna cewa mutum ne da aka nada da yawun gwamnan jaha kuma ana iya tsige shi a ko yaushe.

Bidiyon tuna baya: Sarkin Kano jami’ in gwamnati ne, zan tsige shi sannan na yi bacci harda munshari – Marigayi Rimi

Bidiyon tuna baya: Sarkin Kano jami’ in gwamnati ne, zan tsige shi sannan na yi bacci harda munshari – Marigayi Rimi
Source: Depositphotos

Rimi ya yi wannan furuci ne a lokacin da gaba ta shiga tsakaninsa da Sarkin Kano na wancan zamanin, wato marigayi Sarki Ado Bayero.

Ya ce: “Ni a iya sanina, Sarkin Kano ba komai bane, ba komai bane, ba komai bane, face wani jami’ in gwamnati. Shi jami’ in gwamnati ne da ke rike da mukamin gwamnati, wanda ake biya da kudaden jama’ a kuma mutum ne da aka nada shi da yawun gwamnan jaha sannan ana iya tsige shi, a kore shi, a dakatar da shi, idan ya aikata wani laifi kuma babu wani abu game da Ado Bayero, Sarkin Kano.

“Idan ya aikata kowani laifi, zamu tsige shi sannan kuma muyi bacci harda munshari."

Idan za a tuna a ranar 1 ga watan Afrilun 1981 ne Rimi ya kirkiri sabbin sarakuna guda hudu da suka hada da Auyo da Dutse da Gaya da kuma na Rano wadanda aka ce dai-dai suke da sarkin Kano.

KU KARANTA KUMA: Tsohon shugaban kasa Abdulsalami Abubakar ya tofa albarkacin bakinsa kan tsige sarki Sanusi da aka yi

Sannan kuma aka bai wa sarakunan Hadejia da Gumel da Kazaure martabar sarakunan yanka.

Gwamna Rimi ya kuma bayyana cewa sarakunan "ma'aikatan gwamnatin ne da ke karbar umarni daga hannun shugabannin kananan hukumominsu."

A ranar 7 ga watan na Afrilun 1981 din, sakataren gwamnatin jihar ya aike wa da Sarki takardar neman bayani kamar haka:

"Gwamnan Kano, Alhaji Abubakar Rimi ya umarce ni na rubuta maka wannan wasika domin bayyana bacin ransa da na gwamnatinsa dangane da yadda kake mayar da martani ga gwamnati. Al'umma na tsammanin za ka mutunta gwamnati kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

“Gwamnati ta fahimci cewa tun lokacin da gwamnatin nan ta hau karaga a 1971, akwai abubuwan da suke nuna rashin biyayya ga gwamnatin jihar Kano... saboda haka, gwamna ya umarce ni da na nemi ka kare kanka a cikin awa 48, sannan ka yi bayani kan dalilin da zai hana a dauki matakin ladabtarwa a kanka."

Bayan aikewa da wannan takardar ta neman bahasi, a ranar 10 ga watan Yulin 1981, 'yan daba suka kai hari kan wasu ma'aikatu da suke ganin na kare muradun gwamnati, inda suka kashe mutum 34 sannan suka kona ma'aikatu kamar gidan Rediyon Kano da gidan Jaridar Triumph.

'Yan dabar sun kuma kashe mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin siyasa, Dr Bala Muhammad wanda a lokacin ya ke rubuta takardar tsige sarkin.

Hare-haren 'yan dabar ya karu a birnin Kano duk da cewa ba a san ran mutane ba hakan ya faru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel