Hajjin 2026: Kasar Saudiyya Ta Yi Gyare Gyare, Ta Tura Tallafi ga Kasashen Musulmi 27
- Mahukuntan Saudiyya sun bayyana sababbin tsare-tsaren da aka bullo da su domin saukaka zirga-zirgar alhazai a lokacin aikin Hajji da Umrah
- Ayyukan sun hada da gyara babbar kofar shiga Makkah, masana’antar Kiswah da kuma cibiyar yankan layya ta Adahi
- Haka nan gwamnatin Saudiyya ta bayyana yadda tabaika naman hadaya zuwa kasashen musulmi 27 a duniya a matsayin tallafin jin mai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Saudi Arabia - Gwamnatin Saudiyya ta bayyana wasu manyan tsare-tsare da ayyuka da ake aiwatarwa domin kara inganta aikin Hajji da Umrah ga miliyoyin alhazai da ke ziyartar kasar a kowace shekara.
Hukumar kula da harkokin yada labarai ta Saudiyya ta shirya rangadi na musamman ga ‘yan jarida na gida da na kasashen waje da ke dauko rahoton aikin Hajjin 2026 zuwa muhimman wuraren addini, tarihi da al’adu a birnin Makkah.

Source: Getty Images
Sabuwar hanyar shiga Makkah
Daily Trust ta ce daya daga cikin manyan ayyukan shi ne tsarin Masar, wanda aka ce an tsara shi domin samar da sabuwar hanyar shiga birnin Makkah tare da rage cunkoso ga alhazai da mazauna yankin.
Wani mai ruwa da tsaki a aikin, Abdullaziz Al-Ghurashi, ya ce aikin ya kai tazarar kilomita 3.5 kuma yana kusa da Masallacin Harami da tashar jirgin kasa ta Haramain.
Ya bayyana cewa aikin ya kunshi manyan hanyoyin masu tafiya a kafa, wuraren ajiye motoci a karkashin kasa da kuma tashoshin bas domin saukaka sufuri da kula da taron jama’a yayin Hajji da Umrah.
A cewarsa, wurin na iya daukar mutane kusan 160,000 a lokaci guda, wadanda yawancinsu alhazai ne.
Gidajen tarihi da ilimin kimiyya
Tawagar ‘yan jaridar ta kuma kai ziyara zuwa Gidan Tarihin Rayuwar Annabi SAW da kuma Gidan Tarihi na Hasumiyar Agogo wanda ake kira Universe Sciences Centre.
Mahukuntan Saudiyya sun bayyana cewa gidan tarihin da ke cikin Hasumiyar Agogon Makkah ya kai hawa 80, inda aka ware benaye hudu domin baje kolin yadda duniya ta fara, tafiyar rana da wata, tsoffin hanyoyin auna lokaci da sauransu.
Yadda ake kera kyallen Kiswah
A masana’antar Kiswah ta Ka’aba, jami’ai sun bayyana yadda ake sarrafa bakin kyallen da ake rufe dakin Ka’aba da shi, cewar rahoton Arab News.
Sun ce ana daukar watanni 10 ana kera Kiswah din ta hanyar sakar hannu daga kwararrun masu sana’ar saka na Saudiyya kafin a sauya ta duk shekara a lokacin Hajji.
Saudiyya na tura nama kasashe 27
Tawagar ta kuma ziyarci cibiyar kula aikin layya ta Adahi inda ake sarrafa dabbobin layya da rarraba naman ga kasashe daban-daban.
Mataimakin shugaban wannan sashe, Siraj Muhammed, ya ce cibiyar na sarrafa kusan dabbobi 300,000 a rana lokacin Hajji, yayin da adadin ke kaiwa kusan 900,000 cikin kwanaki ukun layya.

Source: UGC
Ya ce aikin na daukar ma’aikata kusan 17,000 tare da raba naman ga kasashe Musulmi 27 a duniya a matsayin tallafin jin kai.
An yi wa maniyyata sata a Makkah
A wani labarin, kun ji cewa wani maniyyaci daga jihar Jigawa ya bayyana cewa an yi masa fashin makudan kudi a birnin Makkah.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya ta gano kuskure, ta yi gyara a sunan da ake kiran Shugaba Bola Tinubu
Dattijon mai suna Baba Katanga daga kauyen Katanga da ke karamar hukumar Kiyawa ya ce ya rasa dala 400 bayan hawa tasi daga Masallacin Harami zuwa otel dinsa.
Rahoto ya nuna cewa wasu alhazan Jigawa uku da suka je aikin Hajjin sun rasa kudade da kayayyaki masu muhimmanci yayin da suka fada tarkon barayi.
Asali: Legit.ng

