‘Za a Fara Harbe Su’: Matakin Gwamnatin Plateau kan Makiyaya Masu Lalata Gona
- Gwamnatin jihar Plateau ta shirya daukar mataki mai tsauri kan makiyaya masu lalata gonakin mutane domin dakile rikicin a yankuna
- Gwamna Caleb Mutfwang, ya ce zai bai wa jami’an tsaro umarnin harbe duk wanda aka kama yana lalata gonakin jama’a a fadin jihar
- Mutfwang ya bayyana cewa kashe mutane saboda satar ko kashe shanu rashin hankali ne, yana mai cewa babu rai da ba ta fi dabba ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya koka game da yadda rikicin manoma da makiyaya ke jawo asarar rayuka da dukiyoyin al'umma.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati za ta dauki tsauraran matakai kan masu lalata gonakin jama’a a fadin jihar wanda ke jawo asarar rayuka da dukiyoyin al'umma.

Source: Facebook
Matakin da Gwamna Caleb ke shirin dauka

Kara karanta wannan
"Ba dai a matsayin rauni ba," Gwamna Radda ya kafa sharadin sulhu da 'yan bindiga
Mutfwang ya bayyana cewa lokacin da ake kama masu irin wadannan laifuffuka ana kai su Abuja domin gudanar da bincike ya wuce gaba daya, cewar RFI Hausa.
Ya ce zai bai wa jami’an tsaro umarnin harbe duk wanda aka kama yana barnata amfanin gona, domin kawo karshen rikice-rikicen da suka addabi yankin wanda ya hada da hare-haren yan bindiga.
A cewarsa, babu wanda ya fi karfin doka, saboda haka duk wanda aka samu yana aikata irin wannan barna zai fuskanci hukunci mai tsauri.
Gwamna ya yi Allah-wadai da rikice-rikicen Plateau
Gwamnan ya kuma yi Allah wadai da kashe mutane saboda rikicin shanu, yana mai cewa babu wata dabba da ta kai darajar ran dan Adam.
Ya bukaci masu kiwo da sauran jama’a su rika sanar da hukumomi idan an sace musu shanu maimakon daukar doka a hannunsu.

Source: Original
Plateau: Gwamnati ta shirya biyan diyya kan shanu
Mutfwang ya ce hukumomi za su taimaka wajen nemo shanun da suka bace ko kuma lalubo hanyoyin biyan diyya idan hakan ta zama dole.
Ya kara da cewa lokaci ya yi da za a kawo karshen rashin tsaro da rikice-rikicen da suka dade suna haddasa tashin hankali a Plateau, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan
An saki sunayen kananan hukumomi 3 da Boko Haram ta tilasta wa biyan haraji a Yobe
Sai dai wasu mutane sun nuna damuwa cewa sabon matakin gwamnati zai iya cutar da wasu bangarori musamman Fulani makiyaya da ake kashewa shanunsu.
Masu sharhi kan harkokin tsaro na ganin cewa wajibi ne gwamnati ta tabbatar da adalci domin kauce wa kara ruruta rikicin da ke faruwa a jihar da lamarin ya ki ci ya ki cinyewa.
Legit Hausa ta yi magana da Bafillace
Wani Bafillace mai kiwon shanu a yankin karamar hukumar Kwami a Gombe ya ce kowa na son zaman lafiya amma irin wannan mataki zai dagula lamura.
Babangida Manu ya ce ba su jin dadi yadda ake kashe masu shanu wanda yana daga cikin abin da ke kara rura wutar.
Amma ya ce matakin gwamnartin kuma ba tare da adalci ba zai kara rura wutar rikici ne madadin dakile ta.
'Yan bindiga sun kashe mutane a Plateau
A baya, an ji cewa adadin mutanen da aka kashe a hare-haren da aka kai wa yankunan ƙaramar hukumar Barkin Ladi ya kai 10, ciki har da ɗan sanda ɗaya.

Kara karanta wannan
Malami ya yi abin kunya, kotu ta kama shi da laifin dirka wa 'yan mata ciki a Kwara
Maharan sun kai hare-haren ne a lokaci guda a yankunan Sabon Layi, Rakung, Gangare, da kuma kusa da babban asibitin garin domin ba su kulawar gaggawa.
Ƙungiyoyin matasa da na makiyaya ta Plateau sun nuna fargaba kan yadda tsaro ke ƙara taɓarbarwa duk da kasancewar jami'an tsaro a yankin.
Asali: Legit.ng