Atiku Ya ‘Bankado’ Shirin Gwamnoni game da Tazarcen Tinubu a Zaben 2027

Atiku Ya ‘Bankado’ Shirin Gwamnoni game da Tazarcen Tinubu a Zaben 2027

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan hadin bakin gwamnoni game da zaben Bola Tinubu
  • Atiku ya zargi APC da gwamnoni da karkatar da kudaden jama’a domin shirye-shiryen yakin neman zaben 2027 na Tinubu
  • Jam’iyyar ADC ta bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa, tana cewa kudaden FAAC ya kamata su je ayyukan raya kasa ba siyasa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya zargi jam’iyyar APC da gwamnoninta da hadin baki kan zaben 2027.

Atiku ya yi zargin cewa ana karkatar da kudaden jama’a domin shirye-shiryen yakin neman zaben 2027 na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Atiku ya zargi gwamnoni da yashe kudi kan zaben 2027
Shugaba Bola Tinubu da Atiku Abubakar. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Atiku ya tabo gwamnoni kan zaben 2027

Rahoton Arise News ya ce Atiku ce ana zargin gwamnati da hadin kai da wasu gwamnoni wajen tura kudaden gwamnati zuwa asusun da ake amfani da su wajen harkokin siyasa.

Kara karanta wannan

Sabani ya bulla APC bayan kifar da mutum 150 yayin tantance masu son takara

Ya bayyana cewa wannan na kara tsananta matsalar tattalin arziki, rashin tsaro da talauci a fadin kasar, yana mai jaddada cewa ‘yan kasa ne ke daukar nauyin sakamakon rashin kyakkyawan tafiyar da kudaden kasa.

A cewarsa, zargin karkatar da kudade na bayyana dalilin da ya sa matsalar tattalin arziki ke kara zurfi, tare da karuwar rikici da rashin jituwa a cikin gwamnonin APC.

Ya ce:

"Gwamnatin APC da Shugaba Tinubu ke jagoranta na hada kai da gwamnonin APC wajen karkatar da kudaden jama’a zuwa wasu asusun musamman domin yakin neman zaben Tinubu na 2027."
Ana zargin gwamnoni da shirin amfani da kudi domin tazarcen Tinubu
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

ADC ta zargi Tinubu da gazawa a jagoranci

Jam’iyyar ADC ta bayyana lamarin a matsayin abin kunya, zalunci da kuma laifi mai tsanani ga al’umma.

ADC ta ce a yayin da talauci da yunwa ke karuwa a Najeriya, gwamnoni na APC suna amfani da kudaden jama’a wajen shirye-shiryen siyasa.

Ta kara da cewa kudaden FAAC da ya kamata a yi amfani da su wajen raya kasa ana karkatar da su zuwa asusun kamfen siyasa domin yakin neman zabe.

Jam'iyyar ta ce tituna na lalacewa, asibitoci ba su da kayan aiki, makarantu kuma ba su da isasshen kudi duk da yawan kudaden da ake samu.

Kara karanta wannan

Kawancen PDP da APM: Gwamna Makinde zai ayyana shiga takarar shugaban kasa a 2027

Ta bayyana cewa wannan lamari ya nuna gazawar shugabanci, inda ake amfani da gwamnati a matsayin hanyar tara kudi don siyasa, cewar ThisDay.

Jam'iyyar ADC ta bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa cikin gaggawa domin gano gaskiyar zargin karkatar da kudaden FAAC.

Atiku ya kadu bayan mutuwar tsohon dan majalisa

A wani labarin, an ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya nuna bacin ransa kan mutuwar Hon. Abba Anas Adamu a hannun masu garkuwa da mutane.

An sace tsohon dan majalisar ne a babban titin Kaduna zuwa Abuja ranar 3 ga Mayu, 2026, inda ya rasu a ranar 12 ga Mayun 2026 duk da kokarin ceto shi.

Atiku ya bayyana faruwar lamarin a matsayin shaida na gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen kare rayukan yan kasar da take mulka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.