Bidiyon lokacin da tsohon Sarkin Kano Sanusi ke yiwa al’umma ban kwana bayan tsige shi

Bidiyon lokacin da tsohon Sarkin Kano Sanusi ke yiwa al’umma ban kwana bayan tsige shi

A yau Litinin, 9 ga watan Maris ne gwamnatin jahar Kano karkashin jagorancin, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta tsige Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II.

Bayan tsige shi sai jami'an tsaro suka mamaye masarautar inda suka hana shige da fice, sannan daga bisani suka kama tsohon sarkin.

An gano bidiyon tsohon Sarki Sanusi na II a filin jirgi inda ya ke bankwana da al'umman mahaifar tasa wacce ya yi kaura daga cikinta.

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Instagram an gano Sanusi tsaye a kofar shiga jirgin sama yana mai yiwa al'umma addu'a.

KU KARANTA KUMA: Dalilai 5 da suka sa Ganduje ya sauke Sarki Muhammadu Sanusi II

An kuma jiyo muryoyin wasu mutane suna yi masa fatan alkhairi, inda suke ihun "Allah ya sauke ka lafiya dan zaki."

Ga bidiyon a kasa:

Sakataren gwamnatin jahar Kano, Usman Alhaj ya sanar da amincewar gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ga tsige Malam Muhammadu Sunusi a matsayin sarkin Kano.

Zuwa yanzu Gwamna Ganduje ya nada tsohon Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin sabon sarkin masarautar Kano, bayan manyan fadawan masarautar masu nada Sarki sun mika sunan Aminun.

A halin da ake ciki, mun ji cewa biyo bayan tsige tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi II mai murabus, diyarsa ta fito a kafar sadarwar zamani ta Twitter tana yin gargadi tare da kashedi ga masu jajanta musu, inji rahoton TheCables.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito diyar Malam Sunusi mai murabus, Yusrah Sunusi ta yi kira ga abokan huldarta a kafar sadarwar zamani ta Twitter da cewa su daina jajanta musu saboda ba mutuwa aka musu ba, kuma basu mutu ba.

Diyar Sarki mai murabus ta bayyana ma abokanta a Twitter cewa: “Ku daina turo min da ‘Innallillahi wa Inna ilayhir raji’un’ da wai ‘Muna muku jaje’ saboda ba mutuwa muka yi ba. Ta yaya ya zamo ma ni ne nake tausan abokaina, ina fada musu Ku yi hakuri.

“Allah ne Ya so, Inshaa Allah hakan yaafi alheri, ku saurare ne domin kuwa zan cajeku kudin tausan da nake muku.” Inji ta.

Sanin kowa ne dai Musulmai na ambaton ‘Innallillahi wa Inna ilayhir raji’un’ ne a duk lokacin da wani musifa ta fada musu, wanda yake nufin “Daga Allah mu ke, kuma zuwa gare shi zamu koma.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng