Bidiyo: Tsuntsu Ya Firgita Trump a White House, Ya Dauka an Kawo Masa Hari
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya firgita yayin da wani tsuntsu ya wuce ta saman shi yana tsaka da bayani a fadar White House
- Donald Trump ya dakatar da bayanin da ya ke yana kallon sama, inda ya bayyana cewa ya dauka wani jirgi maras matuki aka harbo
- Hakan na zuwa ne yayin da Amurka ke takun saka da kasashen duniya da dama da suka hada da Iran, Venezuela, China da sauransu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban kasa Donald Trump ya shiga wani yanayi a lokacin da wani tsuntsu ya wuce ta saman shi a fadar White House.
Trump ya nuna damuwa, inda ya dakatar da wani muhimmin bayani da ya ke nan take, ya fara dubawa ko hari aka kawo masa.

Source: Getty Images
Rahoton Metro UK ya nuna cewa kasashe da dama na hada jirage masara matuka a wannan zamanin, abin da ya kara tayar da hankalin Trump.
Tsuntsu ya firgita Donald Trump
Shugaba Trump ya yi ihu yana cewa “Oh, oh” bayan ya kalli wani tsuntsu da ya dauka harin jirgi marar matuƙi aka kawo a Fadar White House.
An bayyana cewa a lokacin, shugaban Amurka, Donald Trump ya firgita matuƙa, inda ya fara duba sararin samaniya domin tabbatar da me ke faruwa.
Ya fara da ihu yana cewa “oh, oh,” sannan ya ƙara da cewa 'na yi zaton jirgi marar matuƙi ne!” lamarin da ya sa ’yan jarida suka yi dariya.
Trump ya kara da cewa:
“A yanzu suna ƙera su kala daban-daban kuma suna iya yin mummunar barna kamar yadda wataƙila kuka ji,”
Shugaba Trump ya dawo cikin hayyacinsa daga baya, inda ya gaya wa mutanen da suka taru su zauna su kuma kwantar da hankalinsu.
Ga bidiyon Trump da shafin World Brief ya wallafa a X:
Dalilin firgitar Trump a White House
Wataƙila shugaban ƙasar ya kasance cikin firgici ne bayan karanta rahoton cewa Russia na tara dubban jirage marasa matuƙa domin harin da za su iya kaiwa a gaba kan kasashen NATO.
Rahotannin sirrin Ukraine da Rasha sun nuna cewa shugaban Rasha, Vladimir Putin ya karkatar da manyan sababbin jiragen FPV daga fagen yaƙin Ukraine zuwa wuraren ajiya tun daga ƙarshen shekarar 2025.

Source: Getty Images
An ce Kremlin na iya tara jirage masu hadari har 130,000, kuma ana hasashen adadin zai kai 200,000 kafin ƙarshen bazara.
Jiragen FPV na da haɗari sosai saboda suna amfani na'ura mai matuƙar sirri, wanda hakan ka iya sa su zama masu wahalar katsewa ta hanyar kariyar lantarki ta NATO.
Isra'ila za ta rabu da Amurka
A wani labarin, mun kawo muku cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce suna shirin rage neman tallafin soja daga Amurka.
Netanyahu ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai a Isra'ila bayan yakin da suka gwabza da Iran na kwana 40.
Amurka na cikin manyan kasashen duniya da ke ba Isra'ila tallafin biliyoyin daloli a bangaren soji domin kara karfi a yankin Gabas ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng

