Uwargida Ta Cinna wa Kishiyarta da Ƴaƴanta 2 Wuta a Kano, Bayanai Sun Fito
- Ana zargin wata Maryam Muhammad da zuba wa kishiyarta, Firdausi aranta fetur tare da kunna musu wuta a jihar Kano
- Firdausi, wadda ba ta kai mako biyu da tarewa a gidan ba, tana karbar magani tare da yaranta a wasu asibitocin Kano
- Mijin matar, Malam Saminu, shi ma ya samu raunuka yayin da yake kokarin ceton iyalansa daga wutar da ke cin jikinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano - An shiga firgici a yankin Hotoro da ke birnin Kano bayan wata mata, Maryam Muhammad, ta banka wa kishiyarta da kananan yara biyu wuta.
Wannan mummunan lamari ya faru ne a unguwar Mai Allo da ke Hotoro da misalin karfe 3:00 na asuba, inda kishi ya rikide ya koma tsantsar rashin tausayi.

Source: Original
Uwargida ta cinna wa kishiyarta wuta a Kano

Kara karanta wannan
Kotu ta yanke hukunci, ta ci tarar wanda ya nemi a rushe babban taron APC na kasa
Jaridar Daily Trust ta ruwaito ɗan uwan matar da aka kona, Buhari Musa Sa’ad, ya bayyana wa manema labarai cewa:
“Mun karbi kiran gaggawa da misalin karfe 3:00 na asuba inda aka sanar da mu cewa kishiyar yayata ta banka mata wuta tare da maigidanta da yaranta.
"Abin bakin ciki shi ne, yayata Firdausi ba ta kai mako biyu da tarewa a gidan ba kafin wannan harin ya faru.”
Majiyoyi sun bayyana cewa, uwargidan ta yi amfani da fetur wajen cinna wa amaryarta da yaranta wuta.
Martar ta dade tana yi wa kishiyarta barazana
Rahotanni sun nuna cewa Firdausi Musa, mai shekaru 28, ta taba kai kukan barazana da cin zarafi da kishiyar take mata kafin wannan daren.
Wata ƴar uwar matar mai suna Rukayya, ta bayyana cewa Firdausi ta bar gidan a ranar da abin ya faru saboda tsananin barazana, amma mijinta ne ya lallaba ta ta dawo ba tare da sanin cewa rayuwar ta da ta yaranta ake nema ba.
Yaran biyu da suka kone, ‘yan shekaru 7 da 3, yara ne da matar ta zo da su daga auren ta na baya, in ji rahoton Channels TV.
A halin yanzu, Firdausi da yaranta suna kwance a asibitin kashi na Dala da kuma asibitin kwararru na Murtala Muhammad, inda ake fafutukar ceto rayuwarsu sakamakon munanan raunuka na konewar da suka samu.

Source: Facebook
Halin da ake ciki a Kano
Maigidan, Malam Saminu, wanda yake sana’ar acaba, shi ma yana karbar magani sakamakon konewa da ya yi a hannu da jiki yayin da yake kokarin kashe wutar domin ceton iyalansa.
Wannan lamari ya tayar da hankulan jama’a a jihar Kano, inda mutane ke kiran jami'an tsaro da su tabbatar da adalci.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano ya faskara.
Sai dai, mazauna yankin sun yi kira ga hukuma da ta dauki tsauraran matakai akan duk matar da aka samu da aikata irin wannan danyen aikin na rashin imani domin ya zama darasi ga sauran mata masu kishi irin na hauka.
Matar aure ta kashe kishiyarta
A wani labari, mun ruwaito cewa, wata matar aure ta faɗa komar ƴan sanda bayan an zarge ta da aika-aika kan abokiyar zamanta a Katsina.
Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta tabbatar da cafke matan auren kan zargin kashe kishiyarta har lahira.
Mijin matan ne dai ya kai rahoton lamarin ga ƴan sanda bayan ya dawo kasuwa ya tarar mummunan abu a gidansa.
Asali: Legit.ng

