Tsohon shugaban kasa Abdulsalami Abubakar ya tofa albarkacin bakinsa kan tsige sarki Sanusi da aka yi

Tsohon shugaban kasa Abdulsalami Abubakar ya tofa albarkacin bakinsa kan tsige sarki Sanusi da aka yi

- Shugaban wani kwamitin yin sulhun a tsakanin tsohon Sarki Muhammadu Sanusi da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano, Abdulsalam Abubakar ya ce sun yi iya kokarin bakinsu domin ganin sun kawo sasanci a tsakanin shugabannin biyu

- Abdulsalam ya nuna alhini kan lamarin tsige Sarki Sanusi da gwamnatin Kano ta yi

- Ya ce ba shi da masaniya ko shugaba Buhari ya sa baki ko a'a

Tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar, wanda shine shugaban wani kwamitin yin sulhun a tsakanin tsohon Sarki Muhammadu Sanusi da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano, da samar da zaman lafiya a Najeriya, ya bayyana cewa sun yi iya kokarin bakinsu domin ganin sun kawo sasanci a tsakanin shugabannin biyu, amma abun ya ci tura.

A wata hira da ya yi da muryar Amurka, Abdulsalami, ya ce duk da yake sun zauna a lokuta mabanbanta da gwamnan jahar Kano da kuma tsohon sarki Sarki Sanusi na biyu, kafin suka yi wani zaman tare da su a lokaci daya, hakarsu bata cimma ruwa ba na neman a sasanta su, har abun ya kai ga tsige Sarkin, kasancewa gwamna ne mai wuka kuma mai nama.

Tsohon shugaban kasa Abdulsalami Abubakar ya tofa albarkacin bakinsa kan tsige sarki Sanusi da aka yi
Tsohon shugaban kasa Abdulsalami Abubakar ya tofa albarkacin bakinsa kan tsige sarki Sanusi da aka yi
Asali: Twitter

Game da batun sa bakin Shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen sulhunta rashin jituwar, tsohon Shugaban kasar ya ce ba shi da masaniya ko shugaba Buhari ya sa baki ko a'a. Kuma cewa idan har ya sa baki da mamaki a kai inda ake yanzu.

KU KARANTA KUMA: Yanzun-nan: Tsohon Sarkin Kano Sanusi ya yi jawabi mai taba zuciya bayan tsige shi daga kujerarsa

Ya kuma yi addu’ a kan Allah ya zaunar da jahar Kano lafiya sannan ya kuma kawar da fitina da kawo sauki, cewa duk abunda Allah ya kaddara babu mai iya canja shi.

A wani lamarin kuma, mun ji ceewa shugaban kungiyar Arewa Youth Organizations ta Matasan Arewacin Najeriya, Murtala Abubakar, ya yi magana game da tsige Sarki da gwamnati ta yi a kasar Kano.

Mista Murtala Abubakar ya bayyana cewa akwai laifin shugaba Muhammadu Buhari wajen wannan mataki da gwamnatin jihar Kano ta dauka na tunbuke Sarkin Birni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng