Sau 3 gwamnatin Kwankwaso na aike wa Sanusi da takardar gargadi - Gwamnatin Kano

Sau 3 gwamnatin Kwankwaso na aike wa Sanusi da takardar gargadi - Gwamnatin Kano

Gwamnatin jahar Kano a ranar Talata, 10 ga watan Maris ta bayar da karin dalilai da suka sanya ta tsige Muhammad Sanusi daga matsayin Sarkin Kano.

Ta ce sau uku gwamnatin tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso na aike wa Sanusi takardar gargadi kan rashin mutunta al’ada.

Kakakin gwamnan Kano, Mista Salihu Yakasai ya yi magana ne a wata tashar radiyo mai zaman kanta ta Rave FM a Osogbo.

Ya ce: “duk matsayin sarki yana a karkashin Gwamna ne a kundin tsarin mulki. Idan aka cire son kai da tausayi daga lamarin, za ku san cewa Sarki ma’aikacin Gwamna ne l. Akwai abubuwan da ake sa ran samu daga sarki kuma daga cikinsu akwai girmama hukumomi kuma yana da iyaka wadanda ya dunga takewa tsawon shekaru uku.

Sau 3 gwamnatin Kwankwaso na aike wa Sanusi da takardar gargadi - Gwamnatin Kano
Sau 3 gwamnatin Kwankwaso na aike wa Sanusi da takardar gargadi - Gwamnatin Kano
Asali: UGC

“A koda yaushe Sanusi na zuwa tarurruka don tattauna lamura don samun yabo. A karshen gwamnatin tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ya dawo da haramta bara a unguwanni sannan a wancan lokacin sai Sanusi ya dunga ba Almajirai wuri a fadarsa, yana ciyar dasu kuma a kan wannan lamari, sai da aka bashi takardar gargadi hudu na kin yi mai biyayya.”

KU KARANTA KUMA: PDP ta yi martani a kan sauke Sanusi II daga karagar mulki

Sai dai kuma Kwankwason ya musanta hakan, inda ya ce "ni ban taba ba Mai martaba sarki wata takardar gargadi ko ma wani abu irin wannan ba".

Haka kuma an tambaye shi game da zargin da ake yi wa magoya bayansa 'yan Kwankwasiyya wajen rura wutar rikici tsakanin Sarki Sanusi da Gwamna Ganduje, nan ma tsohon gwamnan ya ce su ba sa goyon bayan kowa sai bangaren gaskiya.

Ya ce a iyakar saninsa kamar yadda "su kansu mutanen gwamnati ke fada", Sarki Sanusi ya gamu da fushin Ganduje ne saboda sun ce basaraken ya ce duk wanda ya ci zabe a Kano, a ba shi nasararsa.

Kwankwaso ya kuma koka kan abin da ya ce wulakancin da aka yi wa jama'ar jihar Kano ta hanyar wulakanta tsohon sarki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel