Sanusi: Gwamnoni na iya tube rawanin kowanene – Fadar Shugaban kasa
Fadar Shugaban kasa ta yi martani ga lamarin tsige Muhammadu Sanusi II daga matsayin Sarkin Kano da gwamnatin jahar ta yi, inda ta bayyana cewa gwamnoni masu ci na iya amfani da karfin mulki kan masarautun da ke a karkashin kulawarsu.
A ranar Litinin, 9 ga watan Maris ne gwamnatin jahar Kano karkashin jagorancin Gwamna Umar Ganduje ta tube rawanin Sanusi, inda aka sanar da mamadin tsohon gwamnan na babban bankin kasar yayinda aka yi gaggawan dauke shi daga jahar.
An tattaro cewa daya daga cikin manyan lauyoyin, Abubakar Mahmoud (SAN), ya ce ana iya janye lamarin.
Da yake martani ga lamarin a ranar Talata, 10 ga watan Maris, Tolu Ogunlesi, daya daga cikin hadiman Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce: “ Gwamna mai ci zai iya tsige kowanene- suna da ikon. Haka tsarin yake. Babu wanda ya wuce a tsige shi. Gwamnoni ne suka nada su, su ke basu ma’ aikata da kuma kudade a ofishoshinsu.”
Ya ce gwamnoni na da iko kan sarakuna a jihohinsu inda ya yi misali da Gwamna Nyesom Wike na jahar Rivers, wanda ya tara sarakunan Rivers kwanaki sannan ya dunga yi masu kamar kananan yara.
Hadimin Shugaban kasar, ya ci gaba da bayyana cewa tsige sarki irin Sarkin Kano ba sabon abu bane, inda ya kara da cewa kaddarar Sanusi ba wai a arewacin kasar bane kawai.
A baya mun ji cewa Tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar, wanda shine shugaban wani kwamitin yin sulhun a tsakanin tsohon Sarki Muhammadu Sanusi da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano, da samar da zaman lafiya a Najeriya, ya bayyana cewa sun yi iya kokarin bakinsu domin ganin sun kawo sasanci a tsakanin shugabannin biyu, amma abun ya ci tura.
A wata hira da ya yi da muryar Amurka, Abdulsalami, ya ce duk da yake sun zauna a lokuta mabanbanta da gwamnan jahar Kano da kuma tsohon sarki Sarki Sanusi na biyu, kafin suka yi wani zaman tare da su a lokaci daya, hakarsu bata cimma ruwa ba na neman a sasanta su, har abun ya kai ga tsige Sarkin, kasancewa gwamna ne mai wuka kuma mai nama.
KU KARANTA KUMA: Yanzun-nan: Tsohon Sarkin Kano Sanusi ya yi jawabi mai taba zuciya bayan tsige shi daga kujerarsa
Game da batun sa bakin Shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen sulhunta rashin jituwar, tsohon Shugaban kasar ya ce ba shi da masaniya ko shugaba Buhari ya sa baki ko a'a. Kuma cewa idan har ya sa baki da mamaki a kai inda ake yanzu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng