Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Kingsley Moghalu, tsohon dan takarar shugaban kasa ya shawarci shugaban Buhari da yayi takatsantsan akan yadda yake gudanar da shari’ar FBI akan Abba Kyari.
Akalla mutane 50,000 ne suka sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da All Progressive Grand Alliance zuwa APC a ranar Alhamis, 29 ga Yuli.
Rahotanni sun nuna cewa Ann Unenge, matar kwamishinan filaye na jihar Benuwai, ta shiga hannun wasu gungun masu dauke da makamai a Makurdi, babbar birnin jihar.
‘Yan majalisa a jihar ta Zamfara sun ce babu wani shiri na tsige mataimakin gwamnan jihar, Mahdi Aliyu Gusau, amma sun nace cewa dole ne ya bayyana a gabansu.
Bello Matawalle a ranar Alhamis, ya yi wa daukacin mazauna Zamfara alkawarin cewa daga yanzu gwamnatinsa za ta dauki tsauraran hukunci kan masu fataucin mutane.
Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi, ya zargi sarakunan gargajiya, ‘yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a kan rashin tsaro da ya addabi kasar nan.
Femi Fani-Kayode, wani jigo a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), da Sanata Shehu Sani sun kaiwa gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ziyara a Abuja.
Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mahdi Aliyu Gusau, a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuli, ya aika wasika ga majalisar dokokin jihar kan zargin shirin tsige shi.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ba da tallafin Naira miliyan 12.8 ga matasa ’yan asalin Jihar su 641 da ake tantancewa domin zama kuratan sojoji.
Aisha Musa
Samu kari