Akwai Matsala: Jigo a APC Ya Hango Abin da Zai Hana Atiku Samun Kuri'un 'Yan Arewa

Akwai Matsala: Jigo a APC Ya Hango Abin da Zai Hana Atiku Samun Kuri'un 'Yan Arewa

  • Obafemi George ya ce sauya sheƙar Abba Atiku Abubakar zuwa APC da goyon bayan Tinubu na sake jefa shakku kan ikirarin Atiku na samun goyon bayan Arewa
  • Jigon na APC ya tambayi yadda Atiku zai samu ƙuri’un masu zaɓe miliyan 25 a Arewa maso Yamma idan ya kasa shawo kan ɗansa
  • George ya kuma yi zargin cewa ’yar shugaban ADC, David Mark, Odon Odon, na neman takarar majalisar wakilai ne a ƙarƙashin tutar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wani mamba a sashen yaɗa labarai na kwamitin kamfen ɗin shugaban ƙasa na APC, Obafemi George, ya yi tambaya kan ikirarin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na samun gagarumin goyon baya a Arewa gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

George ya danganta tambayar tasa da sauya sheƙar ɗan Atiku, Abba Atiku Abubakar, zuwa jam’iyyar APC, inda yake goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: ADC ta bayyana matsayarta kan takarar Atiku duk da hukuncin kotu

An yi magana kan takarar Atiku
Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

George ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamban 2016.

A cewarsa, rashin nasarar Atiku wajen shawo kan ɗansa ya goyi bayan takararsa na jefa tambaya kan yadda zai samu amincewar miliyoyin masu zaɓe a yankin.

APC ta yi tambaya kan tasirin Atiku a Arewa

Ya ce akwai shakku kan ikirarin Atiku na cewa zai samu ƙuri’u daga Arewa maso Yamma, musamman idan aka yi la’akari da cewa ɗansa ya koma APC kuma yana kamfen ɗin Tinubu.

“Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, yana alfahari da cewa Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas za su zaɓe shi, alhali ɗansa na cikinsa ya bar jam’iyyarsa, ya koma APC kuma yana kamfen ɗin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
“To, idan Atiku Abubakar ya kasa shawo kan ɗansa na cikinsa ya yarda da ƙwarewarsa ta jagorantar Najeriya, ta yaya yake tunanin masu zaɓe miliyan 25 a Arewa maso Yamma za su amince da shi?” In ji shi.

Kara karanta wannan

Tsohon na kusa da Atiku ya zayyano matsalolin dan takarar na ADC a 2027

Ya yi magana kan ’yar shugaban ADC

George ya kuma yi tambaya kan amincin wasu mambobin African Democratic Congress (ADC) ga jam’iyyar, inda ya kawo batun siyasar ’yar shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata David Mark.

Ya yi iƙirarin cewa ’yar Mark, Odon Odon, wadda ke neman takarar kujerar Majalisar Wakilai ta tarayya mai wakiltar Otukpo/Ogbadibo/Ohimini a jihar Benue, tana neman takara ne a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

"Abu na biyu, shugaban ADC, Sanata David Mark, shi ma ’yarsa ta cikinsa a Benue, Odon Odon, tana neman takarar kujerar Otukpo/Ogbadibo/Ohimini a Majalisar Wakilai.
“Ku yi tunanin daga wace jam’iyya take neman takara? APC. Idan shugaban jam’iyya ya kasa shawo kan ’yarsa ta ci gaba da kasancewa a jam’iyyarsa, me ya sa ’yan Najeriya za su yarda cewa suna da wani shiri?” In ji shi.
Jigo ya yi magana kan takarar Atiku a 2027
Alhaji Atiku Abubakar na jawabi a wajen taro Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

ADC ta yi magana kan takarar Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar ADC ta dage cewa Atiku Abubakar zai tsaya takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027, duk da hukuncin kotu da ya soke takararsa.

ADC ta yi iƙirarin cewa Atiku zai samu gagarumar nasara a zaɓen, duk da ƙalubalen shari’a da ya dabaibaye shugabancinta da shirye-shiryenta na zaɓen mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng