Da dumi-dumi: EFCC ta kama Saraki kan sabbin zarge-zargen cin hanci da rashawa

Da dumi-dumi: EFCC ta kama Saraki kan sabbin zarge-zargen cin hanci da rashawa

  • Hukumar EFCC ta cafke tsohon shugaban majalisar Dattawa, Bukola Saraki, a yau Asabar, 31 ga watan Yuli
  • EFCC na tuhumar Saraki kan wasu biliyoyin nairori da aka wabcewa daga asusun gwamnatin Kwara a lokacin da yake gwamnan jihar
  • An tattaro cewa an karkatar da kudaden ne zuwa wasu asusun karya waɗanda mallakin Saraki ne a ɓoye

Jihar Kwara - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta tsare tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, bisa zargin sata da handame kudade.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an tsare Saraki, tsohon gwamnan jihar Kwara a ranar Asabar, majiyoyin da suka san ci gaban sun ce, lamarin ka iya haifar da wani tashin hankali ga dan siyasar.

Da dumi-dumi: EFCC ta kama Saraki kan sabbin zarge-zargen cin hanci da rashawa
Hukumar EFCC ta cafke Saraki kan sabbin zarge-zargen cin hanci da rashawa Hoto: The Sun
Asali: UGC

A matsayinsa na shugaban majalisar dattawa tsakanin 2015 zuwa 2019, Mista Saraki ya dauki lokaci mai tsawo yana fuskantar zargin cin hanci da rashawa da bayyana kadarorin karya. Kotun koli ta wanke shi a watan Yunin 2018.

Kara karanta wannan

Hukumar hisbah ta damke wani mai kyamis da ke lalata da mata a Kano

Sai dai kuma, a cikin sabon shari’arsa da EFCC, Premium Times ta ruwaito cewa, Saraki zai amsa tambayoyi kan zargin sata da wawure dukiyar jama'a ta hanyar wasu kamfanoni da asusun bad-da-kama.

Jaridar ta ce akwai wasu kamfanoni da asusun bad-da-kama da Saraki ya rika amfani da su ana jibga masa kuɗaɗe a ciki shi kuma yana ɗiba ya na shagalin sa da su, wanda kuma kuɗaɗe ne na jama’a a lokacin yana gwamna.

An kuma tattaro cewa kudaden sun zarce tunanin mutum domin sun kai daruruwan miliyoyin nairori da kuma dubban daruruwan kudaden waje da ake kwashewa ana danƙarasu cikin wasu ɓoyayyun asusu.

Har ila yau, an ruwaito cewa masu binciken cin hanci da rashawa sun samu jerin sunayen kamfanonin da abin ya shafa tare da yin nazari kan tsarin mu'amalar da ake zargi tsakaninsu da Saraki.

EFCC Ta Kwamushe Tsohon Gwamnan Kwara da Zargin Karkatar da Kudi

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta nemi a dauki tsatsauran mataki kan masu safarar mutane da sauransu

A wani labari na daban, Legit.ng ta kawo a baya cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta kama tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed.

Wasu majiyoyi a hukumar sun fada wa gidan Talabijin na Channels cewa wasu gungun ma’aikata ne suka gurfanar da tsohon gwamnan a hedkwatar EFCC da ke yankin Jabi a Abuja, babban birnin kasar.

An ce ya isa hedikwatar EFCC da misalin karfe 10 na safiyar Litinin, a kan amsa gayyatar da hukumar ta yi masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel