Ki gamsar da mijinki a ko’ina a cikin gidan, ki je gare shi a duk sanda ya bukata: Uwa ga ‘yarta a bidiyo

Ki gamsar da mijinki a ko’ina a cikin gidan, ki je gare shi a duk sanda ya bukata: Uwa ga ‘yarta a bidiyo

  • Wata uwa ta cire kunya ta shawarci ‘yarta kan yadda za ta dunga gamsar da mijinta a koda yaushe
  • Uwar ta ce kafin ma mijin ya neme ta, ya zama dole ta zama a cikin shiri domin ta faranta masa a ko’ina a cikin gidansu
  • 'Yan Najeriya da yawa sun mayar da martani kan bidiyon, sun ce yin hakan ba zai hana mutumin da yayi nisa daga bata ba

Wani bidiyo da ke nuna uwa tana shawartar ‘yarta da za ta je gidan miji a matsayin sabuwar amarya ya haddasa cece-kuce a yanar gizo.

Ba tare da rage komai ba, mahaifiyar amaryar ta ce ta rika nuna masa soyayya ta fannin auratayya a duk lokacin da ya so ba tare da ta hana shi ba.

Ki gamsar da mijinki a ko’ina a cikin gidan, ki je gare shi a duk sanda ya bukata: Uwa ga ‘yarta a bidiyo
Shawarar uwar ya haddasa cece-kuce Hoto: Asiyah Aisha Alubankudi
Asali: Facebook

Ta faɗi gaskiya

A gaban sauran mutane, ta ce za su iya yi a ko'ina a cikin gidan har hakan ya kwanta masu a rai su duka.

Kara karanta wannan

Matar da ta haifi yara 9 a lokaci guda ta magantu, ta ce suna sa ‘pampers’ 100 da shan madara lita 6 a kullun

Mahaifiyar ta yi addu'ar cewa za ta iya daukar dawainiyar gamsar da mijinta a duk lokacin da suke tare a matsayin mata da miji.

‘Yan matan da ke wurin sun yi ta dariya game da kalaman uwar. Ta fuskance su sannan kuma ta yi addu’a, tana rokon Allah ya ba mata abokan zamansu.

Kalli bidiyon a kasa:

Legit.ng ta tattara wasu daga cikin martanin a ƙasa:

Hammed Hammed Babatunde ya ce:

"Shi ya sa nake yaba wa matan da ke ilmantar da mutane a kan auratayya. Mutane na yi musu mummunar fahimta amma a halin yanzu yawancin matan aure ba su da ƙarfin gamsar da miji."

Olori Mofola Luli ta ce:

"Kuma gamsar da shi ya kamata ya hana shi yaudara? .... Shawarar da yakamata su ba mutane biyu ana ba mutum ɗaya kaɗai!"

Tko Ajayi ta ce:

"Idan kin so ki mayar da kanki kasa, idan mutum ya kasance kare, zai ci gaba a haka! A gare ni, shawarata za ta bambanta saboda aure ba batun jima'i kaɗai ba ne! Mutumin zai ji wannan kuma Allah Ya taimaki yarinyar idan miji yana son jima'i! Ta ki ta same ki. "

Kara karanta wannan

Amina ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda yana shan sigari a dakinta, shi kuma ya nemi ta yi masa sabon aure

Kyawawan hotunan ‘yar Najeriya da ta yi wuf da wani Bature, jama’a sun yi cece-kuce

A wani labarin, wata baiwar Allah ta hadu da cikar burinta a wurin wani dan kasar waje kuma sun yi aure a kwanan nan.

Matar mai suna Remy ta shiga daga ciki da burin zuciyarta wanda ya kasance Bature.

A cikin hotunan da shafin @gossipmillnigeria ya wallafa a Instagram, an gano ma’auratan sanye da kaya iri daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel