Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da matar kwamishina a jihar Binuwai
- Wasu 'yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da Ann Unenge, matar kwamishinan filaye na Benuwai
- An sace matar ne da yammacin ranar Alhamis, 29 ga watan Yuli, da karfe 6:00 na yamma yayin da take tuki a motarta
- Sai dai kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Kate Sewuese Anene bai tabbatar da wannan mummunan lamarin ba a daidai lokacin kawo rahoton
Wasu rahotanni masu tayar da hankali sun nuna cewa Ann Unenge, matar kwamishinan filaye na Benuwai, ta shiga hannun wasu masu garkuwa da mutane a Makurdi, babban birnin jihar.
Wani dan uwan Unenge ya fadawa jaridar The Nation cewa an sace ta ne da yammacin ranar Alhamis, 29 ga watan Yuli, da karfe 6:00 na yamma.
An tattaro cewa an yi garkuwa da matar yayin da miyagun suka kuma sace sabuwar motarta kirar Toyota Highlander wacce take tukawa a ranar da abun ya faru.
An ce 'yan bindigar sun yi harbe-harbe da yawa a sama don tsoratar da masu tafiya a kan hanyar yayin da suka tsere da ita zuwa inda ba a sani ba.
Har yanzu mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a jihar, Kate Sewuese Anene bai tabbatar da wannan mummunan lamarin ba.
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon dan majalisar dokokin Jigawa, Haladu Bako
A wani labarin kuma, mun kawo cewa ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wani tsohon dan majalisar dokokin jihar Jigawa, Haladu Bako.
An yi garkuwa da Mista Bako ne a daren ranar Laraba yayin da yake tafiya daga Kano zuwa jihar Jigawa, Mansur Ahmed, mai taimaka wa tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido kan harkokin yada labarai ya bayyana.
Mista Ahmed ya bayyana cewa Mista Bako ya wakilci karamar hukumar Auyo a majalisar jihar daga 2007 zuwa 2015.
Asali: Legit.ng