Masari: Ba na farin ciki da mulkin Katsina saboda rashin tsaro

Masari: Ba na farin ciki da mulkin Katsina saboda rashin tsaro

  • Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya nuna damuwarsa matuka kan yanayin rashin tsaro a jihar
  • Masari ya bayyana cewa baya farin ciki da kasancewarsa gwamnan jihar duba ga yadda abubuwa ke kara tabarbarewa a kullun
  • Gwamnan ya ce sam baya iya yin bacci da daddare sabida damuwa

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya ce ba ya jin dadin mulkin jihar saboda annobar rashin tsaro.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Mista Masari, wanda ya yi magana a ranar Juma'a a wata hira da aka yi da shi, ya ce yanayin tsaro na jiharsa na hana shi bacci.

Masari: Ba na farin ciki da mulkin Katsina saboda rashin tsaro
Masari: Ba na farin ciki da mulkin Katsina saboda rashin tsaro Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Ya ce:

“A cikin wannan mawuyacin lokaci da rashin tabbas, lamarin tsaro duk ya mamaye batun shugabanci daga safe zuwa dare. Ina samun rahotannin tsaro a kowane lokaci ta hanyoyi da yawa a kullum."

The Cable ta nakalto gwamnan ya bayyana matakin rashin tsaro na Katsina a matsayin abin firgitarwa, yana mai jaddada cewa:

"Babu wani shugaba mai hankali da ke da tunanin mutanensa a zuciya da zai yi farin ciki a irin wannan yanayin.
“Yin mulki a wannan mawuyacin lokaci ban ga wani abun farin ciki da mutane ke cewa muna morewa ba.
"A cikin irin wannan yanayin bama yin barcin dare. Kana da 'yan awanni kadan don yin bacci tare da wayarka a ƙarƙashin kunnuwanka kuma duk wanda ya kira ka da tsakar dare ba zai yi hakan don gaishe ka ba illa don gaya muka matsala da ke faruwa.
“Mutane na yi mana mu gwamnoni mummunan fahimta a matsayin mutane da ke more kansu. Wasu mutane suna hasashen abubuwa ne kawai kuma dole ne mu ɗauki abin da muke tsammanin daidai ne saboda idan wani baya cikin tsarin, ba zai iya fahimtar yanayin ba.
“Abin haushin wannan rayuwa shi ne yadda ake yi wa gwamna rakiya tare da kururuwar siren haka ake kai mai laifi gidan yari, mataccen da ke cikin motar daukar marasa lafiya da jami’an kashe gobara duk suna amfani da siren. Don haka menene farin ciki game da siren?” Mista Masari ya tambaya.

"Abu mafi mahimmanci game da shugabanci shine cewa da zarar kun kasance kan madafun iko, koyaushe ku shirya tafiya. Bai kamata ku yarda girman kan mulki ya dauke ku ba,” in ji gwamnan.

Gwamna Masari na Katsina ya bayyana mafita ga matsalar rashin tsaron Najeriya

A wani labarin, Aminu Masari, gwamnan jihar Katsina, ya ce ilimi na iya zama maganin 'yan ta'adda dake addabar kasar nan, The Cable ta ruwaito.

Gwamnan ya yi kira da a sanya hannun jari mai yawa ga ilimtar da matasa da ci gaba a matsayin wata hanya ta magance rashin tsaro a Najeriya.

Masari ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da Ibrahim Musa-Kalla, sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan jihar, ya fitar a ranar Lahadi, 24 ga watan Yuli, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel