Hukumar hisbah ta damke wani mai kyamis da ke lalata da mata a Kano

Hukumar hisbah ta damke wani mai kyamis da ke lalata da mata a Kano

  • Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta tabbatar da kama wani mai sana’ar shagon sayar da magunguna mai suna Yahata Zakari
  • An kama Zakari ne bisa zargin amfani da wani gida sabanin kyamis din wajen lalata da mata
  • An yi kamen ne bayan mazauna yankin sun kai kararsa kan zargin

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wani Yahaya Zakari bisa zargin kai wata mata gidansa da ke Sabuwar Gandu a birnin Kano, jaridar Punch ta ruwaito.

Babban kwamandan hukumar, Dakta Haruna Ibn-Sina, ya tabbatar da kamun a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano ranar Juma’a.

Hukumar hisbah ta damke wani mai kyamis da ke lalata da mata a Kano
Hukumar hisbah ta kama wani mai kyamis da ke lalata da mata a Kano Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Jaridar Aminiya ta kuma ruwaito cewa mazauna unguwar dai sun yi zargin cewa mutumin ya jima yana aikata ta’asar inda ya ware gidan wanda babu kowa a ciki yana kai mata da nufin zai duba su a ciki.

An mika kwafin sanarwar, wacce Malam Lawal Ibrahim, jami’in hulda da jama’a na hukumar ya sa wa hannu, ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta nemi a dauki tsatsauran mataki kan masu safarar mutane da sauransu

A cewarsa, an yi kamen ne bayan rahotanni daga mazauna yankin.

"Matar ta je siyan magunguna daga kyamis din Zakari lokacin da ya kai ta gidansa," in ji shi.

Ibn-Sina ya nuna rashin jin dadinsa kan lamarin da ake zargin mutumin da shi, inda ya tabbatar da cewa hukumar za ta gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Don haka ya shawarci iyaye da su sanya ido sosai kan zirga -zirgar ‘ya’yansu, musamman yara mata, don hana aukuwar abubuwan da ba a so.

Hisbah: An kwamushe wasu mutane da ake zargin suna aikata luwadi a jihar Kano

A wani labari na daban, hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da aikata luwadi a unguwar Sheka Barde a karamar hukumar Kumbotso.

Shugaban hukumar Harun ibn-Sina ne ya tabbatar da kama mutanen cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, BBC ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin Kabilanci: Gwamnatin Gombe ta sanya dokar ta-baci a wasu yankuna 7

Legit.ng Hausa ta tattaro, a cewar sanarwar wasu mazauna yankin ne suka shigar da kara kan wannan batu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng