Bidiyo: Putin Ya Tafi da Jakar Nukiliya yayin da Zai Gana da Trump a China

Bidiyo: Putin Ya Tafi da Jakar Nukiliya yayin da Zai Gana da Trump a China

  • An ga wani jami’in sojan ruwan Rasha dauke da jakar makaman nukiliya ta kasar gabanin taron shugabannin Rasha, Amurka da China
  • Jakar mai suna Cheget na bai wa manyan jami’an Rasha damar ba da umarnin harba makaman nukiliya daga nesa a duk inda suke
  • Ana sa ran shugabannin kasashen uku za su tattauna yakin Iran da Ukraine da kuma batun makaman nukiliya a yau Alhamis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCt, Abuja – Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya nuna jakar umarnin harba makaman nukiliya ta kasarsa gabanin ganawarsa ta farko da takwarorinsa na Amurka da China, Donald Trump da Xi Jinping, a wani taro na musamman.

An dauki hoton wani jami’in sojan ruwan Rasha dauke da jakar Cheget a ranar da ta gabaci ganawar shugabannin uku, wadda aka shirya gudanarwa a gefen taron hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen Asiya da tekun Pasifik (APEC) a birnin Shenzhen na China.

Kara karanta wannan

An tona asirin Amurka kan makaman da ta kawo harin Sokoto da su a 2025

Xi Jinping, Vladimir Putin da shugaba Donald Trump
Shugabannin Amurka, Rasha da China a wajen taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Abin da ke cikin jakar nukiliyar

Al Jazeera ta rahoto cewa Jakar Cheget, wadda aka sanya wa suna daga wani dutse da ke yankin tsaunukan Greater Caucasus, na daga cikin na’urorin da ke ba manyan jami’an Rasha damar ba da izinin amfani da makaman nukiliya daga nesa.

A al’adance, wani jami’in sojan ruwa ne ke dauke da jakar, kuma ana tabbatar da cewa tana kusa da shugaban kasar a duk lokacin da yake gudanar da ayyukansa.

Ba kasafai ake daukar hoton jakar a fili ba, amma a wannan karon gidan talabijin na kasar Rasha mai suna Russia-1 ya nuna ta a wani faifan bidiyo da aka yada sosai a kafafen sada zumunta.

A cikin bidiyon, wani dan jarida ya nuna jakar ga abokin aikinsa, inda ya ce ga jakar makaman nukiliyar da ake magana a kanta.

Daga nan ne wani dan jaridar ya tambayi jami’in sojan ruwan ko jakar da yake dauke da ita ce ta makaman nukiliya, inda jami’in ya amsa da murmushi cewa ita ce.

Kara karanta wannan

Muhimmin tarihi da Tinubu ya kafa game da yaki da ta'addanci a Najeriya

Rasha ta taba nuna jakar a 2023

Rahoton Yahoo News ya nuna cewa wannan ba shi ne karon farko da kafafen yada labaran Rasha suka nuna jakar Cheget a bainar jama’a ba.

A shekarar 2023, lokacin da Putin ya gana da Xi Jinping a birnin Beijing, an dauki hotonsa yana tafiya tare da wasu jami’an sojan ruwa, daya daga cikinsu na dauke da jakar.

A lokacin, wasu wakilan kafar dillancin labaran Rasha ta RIA Novosti sun bayyana cewa akwai wasu jakunkuna da ba za a iya tafiyar shugaban kasar ba tare da su ba.

Haka kuma, a shekarar 2019, gidan talabijin na kasar Rasha mallakar gwamnati mai suna Zvezda ya nuna tsohuwar jakar makaman nukiliya, inda aka ga wasu maballai masu launuka daban-daban a cikinta.

Vladimir Putin
Vladimir Putin a kasar Rasha. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jirgin Rasha ya yi hadari

A wani labarin, mun rahoto cewa wani jirgin saman sojin Rasha ya yi hatsari a yankin Siberia, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dukkan mutane 19 da ke cikinsa.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun tarwatsa gangamin APC a Borno, sojoji sun kai dauki

Ma’aikatar tsaron kasar ta bayyana cewa jirgin kirar An-12 ya yi hatsarin ne yayin gudanar da wani jirgin da aka tsara, a wani yanki da babu mutane a cikinsa na jihar Kemerovo.

Ma’aikatar ta ce binciken farko ya nuna yiwuwar matsalar fasaha ce ta haddasa hatsarin. Gwamnan jihar, Ilya Seredyuk, ya ce jami’an agaji sun kashe gobarar da ta tashi bayan hatsarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng