Janar Buratai Ya Bayyana Abu 1 da Zai Kawo Karshen Ta'addanci a Najeriya
- Tukur Buratai ya ce amfani da makamai kaɗai ba zai kawar da ta’addanci ba, inda ya buƙaci gwamnati ta zuba jari sosai a fannin ilimi
- Tsohon hafsan sojojin ya bayyana cewa ilimi mai inganci da damar karatu ga kowa na da muhimmanci wajen magance matsalolin da ke haifar da ta’addanci
- Buratai ya sanar da shirin bayar da cikakken tallafin karatu ga waɗanda suka yi nasara a gasar rubuce-rubuce cikin shekaru uku zuwa biyar masu zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Nasarawa - Tsohon hafsan sojojin kasa na Najeriya (COAS), Laftanar Janar Tukur Buratai mai ritaya, ya bayyana cewa ƙarfin soji kaɗai ba zai iya kawo ƙarshen ta’addanci ba.
Janar Buratai ya buƙaci gwamnati ta zuba jari sosai a fannin ilimi domin haɓaka tunanin matasa da basirarsu, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen yaƙi da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro a dogon lokaci.

Kara karanta wannan
Mazan fama: Amurka ta yabawa sojojin Najeriya bayan gudanar da wani gagarumin aiki

Source: Facebook
Jaridar TheCable ta ruwaito cewa Buratai ya bayyana hakan ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamban 2026 a wajen bikin bayar da kyaututtukan gasar adabin matasa ta shekarar 2026.
An kuma ƙaddamar da kundin rubuce-rubucen da aka tattara na shekarar 2025 na shirin adabi mai suna T.Y. Buratai Literary Initiative (TYBLI), a jihar Nasarawa.
Me ya ce kan ta'addanci?
Tsohon hafsan sojojin ya ce bai kamata a dogara da ƙarfin soja kawai wajen magance matsalolin tsaro ba. Ya jaddada cewa ilimi mai haɗa kowa da kuma faɗaɗa damar samun karatu na da muhimmanci.
A cewarsa, irin waɗannan matakai za su taimaka wajen magance yanayin da ke ba ta’addanci da tsattsauran ra’ayin tashin hankali damar yaɗuwa a Najeriya.
Buratai ya bayyana muhimmancin ilimi da waɗannan kalamai:
“Bindiga na iya kashe ɗan ta’adda, amma ilimi kaɗai ne zai iya kashe ta’addanci.”
Ya ce ci gaban ƙasa bai kamata ya tsaya kan gine-gine, ƙarfin soji da albarkatun tattalin arziki kawai ba.

Kara karanta wannan
APC ta bayyana gaskiyar da ta yarda da ita kan matsalar rashin tsaro a gwamnatin Tinubu
A maimakon haka, ya kamata a haɗa da haɓaka ilimin al’umma, ƙwarewar tunani, ƙirƙira da kuma fahimtar kyawawan ɗabi’u.
Ya ƙara da cewa wajibi ne a bai wa matasan Najeriya, ba tare da la’akari da asalinsu ba, dama da ƙarfafa gwiwa domin su haɓaka basirarsu da bayar da gudummawa ga ci gaban al’umma.
Buratai ya yi kira ga jami’o’i
Tsohon hafsan sojojin ya ce an kafa shirin TYBLI ne bisa imanin cewa ƙasashe masu ci gaba ba sa dogara da ƙarfafan sojoji da tattalin arziki kawai.
Ya bayyana cewa tunani mai zurfi, adabi da kuma al’umma mai ilimi na daga cikin ginshiƙan gina ƙasa mai ƙarfi.
Janar Buratai ya buƙaci jami’o’i su ƙara mayar da hankali kan adabin matasa ta hanyar bincike, koyarwa da shirye-shiryen da za su bunƙasa ƙirƙira da tunani mai zurfi.
“Makarantar da ke samar da ɗalibai masu kyakkyawan sakamako a jarabawa, amma ta yi watsi da ƙirƙira da tunani mai zurfi, ba ta shirya ɗalibanta yadda ya kamata domin fuskantar makomar rayuwa ba.” In ji shi.
Ya bayyana cewa tun daga shekarar 2023, shirin TYBLI ya samar da dama ga matasan Najeriya daga sassa daban-daban domin nuna basirarsu a fannin rubuce-rubuce.
A cewarsa, shirin ya taimaka musu wajen sauyawa daga kasancewa masu karanta littattafai kawai zuwa zama marubuta masu ƙirƙirar nasu ayyukan adabi.

Source: Facebook
Buratai ya magantu kan kudin makamai
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Yusuf Buratai (Mai ritaya), ya bayyana cewa dala biliyan 1 da gwamnatin tarayya ta amince da warewa domin sayen makamai a lokacin da yake ofis.
Janar Buratai ya ce majalisar tattalin arziki ta kasa (NEC) ce ta amince da kudin, amma bai bi ta hannunsa ko asusun rundunonin sojin kasa, ruwa da sama ba.
Asali: Legit.ng
