Yahaya Bello Ya San Makomarsa, Kotu Ta Yi Hukunci kan Takararsa Ta Sanata

Yahaya Bello Ya San Makomarsa, Kotu Ta Yi Hukunci kan Takararsa Ta Sanata

  • Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da aka shigar domin kalubalantar nasarar tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello
  • Mai shari’a Inyang Ekwo ya ce Momoh Obaro bai fara amfani da hanyoyin warware rikicin cikin APC ba kafin kai karar kotu
  • INEC ta tabbatar da cewa Bello ne ya lashe zaben fidda gwani da kuri'u 72,999, yayin da Obaro ya zo na uku da kuri'u 188

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Babbar kotun tarayya ta yi watsi da karar da aka shigar domin kalubalantar zaben fitar da gwani da jam’iyyar APC ta gudanar.

Kotun ta tabbatar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a matsayin dan takararta na kujerar sanatan Kogi ta Tsakiya a zaben 2027.

Yahaya Bello ya yi nasara a kotu
Tsohon gwamnan Kogi mai neman kujerar sanata, Yahaya Bello. Hoto: Alhaji Yahaya Bello.
Source: Facebook

Alkalin ya ce karar ta kasance wadda aka shigar tun kafin lokacin da ya dace, saboda haka ta zama ba ta kai matsayin da kotu za ta saurare ta ba, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Siyasar Arewa: Kotu ta dawo da tsohon gwamnan APC, zai yi takarar sanata

A hukuncin da ya yanke ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamba, 2026, mai shari’a Inyang Ekwo ya bayyana cewa mai karar, Momoh Obaro, bai bi hanyoyin da APC ta tanada domin warware rikice-rikicen cikin gida ba kafin ya garzaya kotu.

Dalilin kotu na yin watsi da karar

Mai shari’a Ekwo ya kuma soki takardun sakamakon zaben fidda gwani da Obaro ya gabatar a matsayin hujja, inda ya ce ba su dauke da sa hannun shugaban kwamitin da sakatarensa da suka gudanar da zaben ba.

Obaro ya shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1085/2026, inda ya bukaci kotu ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na APC da aka gudanar ranar 18 ga watan Mayun 2026.

Ya kuma bukaci kotu ta umarci APC ta mika sunansa ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a matsayin dan takararta, tare da hana jam’iyyar mika sunan Bello ga hukumar.

Kara karanta wannan

Kotu ta shiga maganar Aminu Gwarzo da 'yan NDC ke neman hana shi takara a Kano

Zargin da Obaro ya yi kan Bello

A cikin rantsuwar da ya gabatar wa kotu, Obaro ya yi zargin cewa ba a tantance Bello ba, balle a ba shi damar shiga zaben fidda gwani.

Ya ce ya yi mamakin jin labarin cewa tsohon gwamnan ne ya lashe zaben, har ma aka mika sunansa ga INEC, cewar TbeCable.

Obaro ya kuma yi ikirarin cewa Bello ya janye takararsa da kansa bayan ya mika fom din nuna sha’awa da na takara ga jam’iyyar.

Ya ce an kai wasikar janyewar takarar ga hukumomin APC da abin ya shafa, kuma Bello bai taba sauya matsayinsa ta hanyar janye wannan wasika ba.

Martanin Yahaya Bello da APC

Sai dai Bello ya musanta zarge-zargen, inda ya dage cewa ya shiga zaben fidda gwani kuma ya samu mafi yawan kuri'un da aka kada.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa Obaro ne ya zo na uku da kuri'u 188, yayin da shi kuma ya samu kuri'u 72,999.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Gobara ta kama a katafariyar ma'ajiyar babban dan kasuwa a jihar Kaduna

Ya kuma ce an tantance shi tare da ba shi damar shiga zaben fitar da gwani.

Bello ya kara da cewa Obaro bai gabatar da sahihin takardar sakamakon zabe da kwamitin da aka kafa bisa ka'ida ya fitar ba.

Abin da INEC ta ce kan zaben

A nata bangaren, INEC ta bukaci kotu ta yi watsi da karar, inda ta bayyana cewa ta sanya ido kan zaben fidda gwanin bisa tanadin doka.

Hukumar ta ce ta tabbatar da Bello a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya samu mafi yawan kuri'u masu inganci a tsakanin 'yan takara uku.

INEC ta kara da cewa rahotannin jami'anta daga kananan hukumomi biyar na mazabar sanatan Kogi ta Tsakiya sun nuna cewa zaben ya bi tanadin dokar zabe ta 2026 a mafi yawan bangarorinsa.

Kotu ta tabbatar da takarar Gabriel Suswam

Mun ba ku labarin cewa mai shari’a Inyang Ekwo ya tabbatar da cewa Gabriel Suswam ne ya lashe zaɓen fitar da gwani na APC da aka gudanar ranar 18 ga Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Bayan Atiku, an samu dan takarar da ake ganin zai kayar da Tinubu a 2027

Kotun ta soke sauya sunan Suswam da APC ta yi, inda ta bayyana matakin a matsayin wanda ya saɓa wa dokokin zaɓe da kundin tsarin mulki.

Ta umarci APC da ta aika sunan Suswam ga INEC a matsayin ɗan takararta na kujerar Sanatan Benue ta Arewa maso Gabas a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.