Da duminsa: Rundunar soji ta saki hotunan yan ta’adda, matansu da yara da suka mika wuya ga sojoji a Borno

Da duminsa: Rundunar soji ta saki hotunan yan ta’adda, matansu da yara da suka mika wuya ga sojoji a Borno

  • Rundunar Sojojin Najeriya sun tsare mayakan Boko Haram da suka mika wuya a karamar hukumar Bama ta jihar Borno
  • Mutanen sun hada da yara, mata da 'yan ta’adda wadanda suka mika kan su ga sojoji a jihar bayan nasarar da suka samu
  • Mai magana da yawun NA, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ya ce an dauki bayanan matan

Bama, Borno - Shugabancin rundunar Sojojin Najeriya ta sanar da gagarumar nasarar da sojojin Bataliya ta 202 suka samu a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun NA wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar, 31 ga watan Yuli a shafin Facebook na rundunar ya ce sojojin sun tsare ‘Yan tawayen da iyalansu, wadanda suka hada da manyan mata 10 da yara 22.

Da duminsa: Sojoji sun saki hotuna yayinda yan ta’adda, matansu da yara suka mika wuya ga sojoji a Borno
An dauki bayanan matan da yaran Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Onyema ya kara da cewa, a wani ci gaban kuma, sojojin na Forward Operational Base (FOB) a karamar hukumar sun kame mayakan Boko Haram 20 da iyalansu da suka hada da manyan mata 15 da yara 26.

Kara karanta wannan

Mayaƙan Boko Haram Da Iyalansu Su 91 Sun Miƙa Wuya a Borno, Rundunar Sojojin Nigeria

Ya yi bayanin cewa wannan nasarar ya biyo bayan ayyukan kakkaba da sojoji ke yi a duk yankin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Onyema ya bayyana cewa an yiwa yaran allurar rigakafin cutar shan inna, yayin da aka dauki bayanan manya da mata da ake zargi kuma a halin yanzu suna gudanar da binciken farko.

Gwamna Zulum ya zabi mazajen mafarauta 1000 domin kare manoma daga Boko Haram

A wani labarin, Babagana Umara Zulum, gwamnan jihar Borno, a ranar Alhamis, ya rantsar da mafarauta 1,000 domin yaki da Boko Haram, The Cable ta ruwaito.

Aikin mafarautan shi ne kare manoman da ke noma albarkatun gona a wajen garin Jere, babban birnin Maiduguri, kananan hukumomin Konduga da Mafa na jihar.

An rantsar da mafarautan ne makonni kadan bayan jami'an tsaro na farin kaya (DSS) da sojojin sun gama tantance su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel