Rashin tsaro a Najeriya: Ministan tsaro Magashi ya bayyana sunayen wadanda za a zarga

Rashin tsaro a Najeriya: Ministan tsaro Magashi ya bayyana sunayen wadanda za a zarga

  • Ministan tsaro Bashir Magashi ya bayyana wasu dalilai da ke haifar da matsalar tsaro a Najeriya
  • Magashi ya ce rashin 'yan siyasa da sarakunan gargajiya a matakin kananan hukumomi na haifar da wani gurbi wanda masu aikata laifi ke amfani da shi
  • Ministan ya kuma yi zargin cewa masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a yankin arewa sun yi sulhu

Awka, jihar Anambra - Manjo Janar Bashir Magashi, ministan tsaro, ya zargi 'yan siyasa, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki kan matsalar rashin tsaro da ke ta'azzara a kasar.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa ministan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuli, a yayin taron kwana daya na tsaro da jami’ar Nnamdi Azikiwe, Awka, jihar Anambra ta shirya.

Rashin tsaro a Najeriya: Ministan tsaro Magashi ya bayyana sunayen wadanda za a zarga
Ministan tsaro Bashir Magashi ya zargi 'yan siyasa, sarakuna da malamai kan rashin tsaro Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa ministan ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman, Ahmed Jibrin a taron.

Kara karanta wannan

Buhari a Landan: Burtaniya ta shirya taimakawa Najeriya a yaki da matsalar rashin tsaro

Ya zargi masu ruwa da tsaki da yin sassauci a kan tsaro.

An ruwaito Ministan yana cewa:

“Masu rike da mukaman siyasa da na gargajiya a matakin kananan hukuma galibi basa kasancewa a mazabunsu don haka suke haifar da gibin da masu tayar da kayar baya,‘ yan ta’adda da ‘yan fashi ke cikawa a cikin mulkin kananan hukumomin.
"Me za a ce game da gazawar shugabanninmu na addini da masu bayyana ra'ayi wadanda ba su yin jawaban jan hankali ga fusatattun masu kishin addini, da kuma ci gaba da hada kan mazauna yankin daga shugabannin yanki da na jama’a?"

Rashin ingantaccen tsarin leken asiri

Ministan ya kuma dora alhakin matsalar tsaro a kan rashin ingantaccen tsarin leken asiri da kuma rashin son yin aiki a kan bayanan da aka bayar, The Guardian ta ruwaito.

Ya kara da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a yankin arewa wanda alamu suka nuna mahara, 'yan fashi da masu garkuwa da mutane sun yi sulhu da su.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Yadda Kotu ta wanke Sheikh Zakzaky da matarsa, ta umarci a sake su

Ya ce:

“Abin da ya fi bayyana a fili shi ne rashin ingantaccen tsarin leken asiri ko kuma rashin son yin amfani da bayanan da aka bayar wajen gudanar da ayyukan tsaro ta bangaren sojoji da hukumomin tsaro, kamar yadda ya nuna dukkan masu ruwa da tsaki a harkar tsaro sun yi sulhu da yan ta’addan a arewa maso gabas da kuma ‘yan fashi / masu satar mutane a Arewa maso yamma da Arewa ta Tsakiya.”

Ya yi kira ga wadanda ke tayar da hankali a kasar da su hanzarta janyewa daga hakan.

Ministan Tsaro Ya Yi Sharhin Kalaman Buhari Na ‘Yaren da Suka Fi Fahimta’

A baya mun kawo cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi daidai da ya ce zai yi maganin masu aikata laifuffukan dake addabar kasar "da yaren da suke fahimta" a cewar ministan tsaron Najeriya, Bashir Magashi.

A cewar ministan tsaron, babu wani aibi don shugaban kasar ya kawar da masu shirin hargitsa kasar, in ji The Cable.

Kara karanta wannan

Labari Da Ɗuminsa: Kotu Ta Tura Sunday Igboho Gidan Yari a Kwatano

Da yake ci gaba da bayani, ya sha alwashin cewa za a hukunta masu aikata laifuka a kasar nan domin doka za ta bi dasu yadda ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel