Gwamna Zulum ya ba da tallafin miliyan N12.8 ga matasa masu neman aikin soja

Gwamna Zulum ya ba da tallafin miliyan N12.8 ga matasa masu neman aikin soja

  • Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ba da tallafin miliyan N12.8 ga matasa ’yan asalin Jihar su 641 da ake tantancewa domin zama kuratan sojoji
  • Za a dunga biyan matasan N15,000 a matsayin alawus duk wata a tsawon lokacin da za su yi a makarantar horas da kananan sojoji
  • Matasan da za su ci gajiyar wannan shiri sun kasance wadanda suka yi nasarar tsallake matakai mabanbanta na gwaje-gwajen lafiyar da sauransu

Rahotanni sun kawo cewa Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya ba da tallafin kudi har miliyan N12.8 ga matasa ’yan asalin Jihar su 641 da ake tantancewa domin zama kuratan sojoji.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa Zulum ya ziyarce matasan ne a Barikin Sojoji na Maimalari da ke garin Maiduguri, babbar birnin jihar Borno, inda ya sa a ba wa kowannensu N20,000.

Gwamna Zulum ya ba da tallafin miliyan N12.8 ga matasa masu neman aikin soja
Zulum ya yi umurnin biyan matasan N15,000 duk wata a matsayin alawus Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Har ila yau gwamnan ba da umarnin biyan kowanne daga cikin matasan N15,000 a duk wata a matsayin alawus a tsawon lokacin da za su kwashe a makarantar horas da kananan sojoji (DEPOT) da ke Zariya.

Matasan su kasance wadanda suka yi nasarar tsallake matakai mabanbanta na gwaje-gwajen lafiyar da sauransu, kuma nan ba da dadewa ba za a kai su Dajin Falgore domin tantancewar karshe, kafin a kai su DEPOT.

Zulum, wanda Kwamandan Rundunar Operation Hadin Kai, Manjo-Janar Christopher Musa ya karbi bakuncinsa, ya yi kira ga matasan a kan su jajirce.

Gwamna Zulum ya gwangwaje sojojin da suka ji rauni da miliyoyin Nairori ranar Sallah

A baya mun kawo cewa Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bai wa sojojin da suka ji rauni da ke yaki a yankin tallafin naira miliyan 10.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya sanar da ba da tallafin ne a yayin liyafar cin abincin rana da babban hafsan sojin kasa na Najeriya Manjo Janar Farouk Yahaya ya shirya a Barikin Maimalari da ke Maiduguri.

Gwamna Zulum ya yaba wa dakarun kan jajircewarsu da kuma jaddada alkawarin gwamnatinsa na ci gaba da ba su goyon baya har a cimma nasara a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel