Mataimakin gwamnan Zamfara ya sa kafar wando daya da ‘yan majalisa, ya ce ba zai gurfana a gabansu ba

Mataimakin gwamnan Zamfara ya sa kafar wando daya da ‘yan majalisa, ya ce ba zai gurfana a gabansu ba

  • Majalisar dokokin Zamfara ta gayyaci mataimakin gwamnan jihar Mahdi Aliyu da ya gurfana a gabanta domin yin karin haske game da lamura
  • Aliyu ya shiga tsaka mai wuya da majalisar jihar saboda ya ki bin sahun maigidansa, Gwamna Bello Matawalle zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC)
  • Mataimakin gwamnan, ya ce ba zai bayyana a gaban majalisar ba tunda ya kai karar ‘yan majalisar

Gusau, Zamfara - Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mahdi Aliyu ya bayyana cewa ba zai amsa gayyatar da majalisar dokokin jihar ta yi masa ba saboda ya kai ‘yan majalisar kara kotu.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa yan majalisar sun ba Aliyu wa’adin awanni 48 ya bayyana a gabanta domin kare kansa daga zargin aikata ba daidai ba.

Mataimakin gwamnan Zamfara ya sa kafar wando daya da ‘yan majalisa, ya ce ba zai gurfana a gabansu ba
Mataimakin gwamnan Zamfara ya ce ba zai gurfana a gaban majalisar dokokin jihar ba Hoto: Mahdi Aliyu.
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa yan majalisar sun zargi Aliyu da rashin tausayin mutanen Zamfara saboda gudanar da taron siyasa a ranar 10 ga watan Yuli, bayan kashe-kashen da yan fashi suka yi a karamar hukumar Maradun ta jihar.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan jihar Zamfara ya koka kan barazanar majalisa na tsige shi

Majalisar dokokin Zamfara ta gayyaci mataimakin gwamna Aliyu

Sun kira shi ne don ya bayyana abin da ya sa ya aikata hakan, cigaban da aka fassara a matsayin mataki na tsige mataimakin gwamnan.

TVC News ta kuma ruwaito cewa, Mahdi, a wata wasika mai kwanan wata Alhamis, 29 ga watan Yuli, wanda ya aika wa Majalisar, ya ce ba zai bayyana a gaban ‘yan majalisar ba har sai an yanke hukunci a kotu.

Ya ce:

“A wannan shari’a da ake jira, ofishin kakakin wannan gida mai girma bangare ne. Bugu da kari, akwai oda da kotu ta bayar a ranar 19 ga Yuli, na cewa a bar komai yadda yake. Duk da yake a shirye nake na amsa gayyatar, amma abin baƙin ciki, ya zama tilas na dakata saboda karar da ke kasa, da kuma umarnin kotu."

Rahoton ya ce bayan amincewa da karbar wasikar a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuli, majalisar ta umarci sashinta na shari'a da ta yi nazari a kanta da takardun kotun.

Kara karanta wannan

Zan Dau Tsattsauran Mataki Kan Jiga-Jigan Siyasa Dake Tada Hargitsi a Jihata, Gwamna

Mataimakin gwamnan jihar Zamfara ya koka kan barazanar majalisa na tsige shi

A baya mun kawo cewa Barista Mahdi Aliyu Muhammad Gusau, ya ce majalisar dokokin jihar na ci gaba da shirin tsige shi a ranar Alhamis duk da cewa hakan ya saba wa doka da umarnin kotu, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake yi wa manema labarai bayani a ofishinsa a ranar Alhamis 29 ga watan Yuli, mataimakin gwamnan ya ce matakin da Majalisar Dokokin jihar ta dauka ya nuna rashin biyayya ga umarnin kotu kuma zai zama daidai da nuna rashin bin doka.

Asali: Legit.ng

Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel