INEC Ta Fito Ta Bayyana Dalilin da Ya Sa ba Ta Cire Sunan Atiku daga Jerin Yan Takara ba
- Hukumar INEC ta yi bayanai kan dalilin da ya sa har yanzu ake ganin sunan Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na ADC a shafinta
- INEC ta ce ba za ta dauki mataki kan rikicin shugabancin ADC ba har sai an kammala shari’ar da ke gaban kotu
- ADC ta daukaka kara zuwa kotun daukaka kara tare da neman dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an yanke hukunci kan karar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi bayanin dalilin da ya sa har yanzu sunan Atiku Abubakar, ke cikin jerin sunayen yan takarar shugaban kasa a shafinta na yanar gizo.
INEC ta tabbatar da cewa har yanzu Atiku ne a matsayin dan takarar shugaban kasa na ADC a babban zaben 2027, duk da wani hukuncin babbar kotun tarayya da ya shafi shugabancin jam’iyyar.

Source: Facebook
Me yasa INEC ta ƙi cire sunan Atiku?
A rahoton Tribune Nigeria, Hukumar ta ce ba za ta dauki wani mataki kan lamarin ba har sai an warware takaddamar shari’ar da ke gudana kan shugabancin ADC baki daya.
Wannan na zuwa ne bayan hukuncin da Mai shari’a Peter Lifu ya yanke a ranar 5 ga Nuwamba, 2026, wanda ya shafi shugabancin jam’iyyar adawa karkashin jagorancin David Mark.
ADC ta kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara, inda ta shigar da kara tare da neman dakatar da aiwatar da hukuncin har sai kotun ta yanke hukunci kan daukaka karar.
Wani babban jami’in INEC, wanda ya zanta da Arise News, ya ce hukumar ba za ta cire sunan Atiku ko daukar wani mataki ba har sai an kammala matakan shari’ar da ke gaban kotu.
INEC ta yi magana kan Nafiu Bala
Jami’in ya kuma nuna shakku kan sanarwar da Nafiu Bala Gombe ya fitar cewa ya koma bakin aikinsa a matsayin shugaban ADC na kasa bisa bin umarnin kotun.
Da aka tambaye shi ko INEC ta samu takarda a hukumance daga Bala Gombe game da ikirarin komawarsa matsayin shugaban ADC, majiyar ta yi tambaya kan yadda hakan zai yiwu ganin cewa har yanzu akwai matakan shari’a da ba a kammala ba.
“Ban san yadda hakan zai yiwu ba, alhali akwai sanarwar daukaka kara da kuma bukatar dakatar da aiwatar da hukuncin. Duk da haka, INEC za ta bayyana matsayarta a kan lokaci,” in ji jami’in.

Source: Facebook
Dangane da dalilin da ya sa har yanzu sunan Atiku ke shafin hukumar, majiyar INEC ta sake tambayar ko Nafiu Gombe yana ganin shi ke da tikitin takarar shugaban kasa na ADC.
Nafiu Bala ya tura wasika ga INEC
Kun ji cewa Nafiu Bala Gombe ya rubuta wa hukumar INEC wasika, yana sanar da ita cewa ya koma kan mukaminsa na shugaban jam’iyyar ADC na kasa.
A wasikar da ya aike wa shugaban INEC ranar 16 ga Nuwamba, 2026, Gombe ya bukaci hukumar ta amince da shi a matsayin shugaban ADC domin dukkan harkokin hukuma, wasiku da takardun jam’iyyar.
Asali: Legit.ng

