Mutane da Dama Sun Mutu da Babbar Mota Dauke da Shanu Ta Gamu da Tsautsayi
- Rahotanni sun ce mutane 14 sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya rutsa da babbar motar DAF da ke ɗauke da shanu 35 da fasinjoji
- Hatsarin ya faru ne a kusa da Ibeto, a kan hanyar Kontagora a jihar Neja da misalin ƙarfe 11 na safe ranar 17 ga Nuwamba, 2027
- ’Yan sanda sun ce ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin hatsarin da kuma kama direban motar da ake zargi ya gudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger, Nigeria - Rahotanni sun bayyana cewa mutane 14 sun mutu a wani hatsarin mota da ya haɗa da babbar motar DAF da ke ɗauke da shanu 35 da wasu fasinjoji a kan hanyar Kontagora da ke Jihar Neja.
An ruwaito cewa hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 11 na safe ranar 17 ga Nuwamba, 2026 kusa da garin Ibeto. Motar mai lambar rajista Lagos AZL 267 XH tana kan hanyarta ne daga Ƙaramar Hukumar Koko ta Jihar Kebbi zuwa Legas.

Source: Original
Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Zagazola Makama ya fitar da rahoton wannan hatsari a shafinsa na X.
Yadda hatsarin ya faru a jihar Neja
Makama ya ce:
“Majiyoyin ’yan sanda sun bayyana cewa wata motar da ba a sani ba, wadda ke tafiya a hannu ɗaya da babbar motar, ta yi ƙoƙarin wuce ta, amma ta goga mata, lamarin da ya sa direban babbar motar ya rasa ikon sarrafa ta kafin ta faɗi.
“An ruwaito cewa direban motar da wasu mutane 13 da ke cikinta sun mutu a wurin da hatsarin ya faru.
Daga cikin waɗanda aka gano sun mutu akwai Umar, mai shekara 45, direban motar daga Kaoje; Anas Suleiman, mai shekara 25, da Sufiyanu Suleiman, mai shekara 40, dukansu daga Koko.
Sauran sun hada da Salim Abu Dogo, mai shekara 30; Abubakar Shehu, mai shekara 45; Yahaya Abubakar, mai shekara 30; da Manu, mai shekara 35, dukansu daga Dankigari da sauransu.
An fara tanyance wadanda suka mutu
Majiyoyin ’yan sanda sun shaida wa Makama cewa ’yan uwa ne suka tantance gawarwakin waɗanda suka mutu, yayin da aka miƙa su domin yi musu jana’iza bisa tsarin addinin Musulunci.
An kuma ajiye gawarwaki biyu da ba a gano ko su waye ba a ɗakin ajiye gawa na Babban Asibitin Kontagora.

Source: Twitter
Makama ya ce:
“Daga baya an gano motar da ake zargin ta yi ƙoƙarin wuce babbar motar a Kaboji, cikin Ƙaramar Hukumar Magama, sannan aka kai ta ofishin rundunar ’yan sanda na shiyya.
“Sai dai rahotanni sun ce direban motar ya gudu, kuma har yanzu ba a kama shi ba.”
A cewar rahoton, rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta ce ana ci gaba da bincike domin gano cikakken abin da ya haddasa hatsarin da kuma kama direban da ya tsere.
Hatsarin mota ya rutsa da ango
Kun ji cewa wani matashi mai suna Abubakar Abdullahi, wanda aka fi sani da Malam Habu, ya rasu a ranar da zai je wajen daurin aurensa a jihar Gombe.
Abokin mamacin ya ce Habu ya rasu ne sakamakon hatsarin mota, lamarin da ya faru yayin da yake kan hanyar zuwa wajen daurin auren nasa.
Asali: Legit.ng

