Kwamitin Shari'a Ya Fitar da Gargadi kan Zaben Najeriya na 2027

Kwamitin Shari'a Ya Fitar da Gargadi kan Zaben Najeriya na 2027

  • Majalisar Koli kan Shari’a a Najeriya ta gargadi ’yan siyasa kan daukar matakan da ka iya haddasa tashin hankali gabanin zaben 2027
  • Majalisar ta ce babu wani burin siyasa da ya kai a rasa rayukan ’yan Najeriya, inda ta bukaci masu ruwa da tsaki su tabbatar da zaman lafiya
  • Ta kuma bukaci ’yan Najeriya da suka cancanci kada kuri’a su mallaki katin zabe tare da kada kuri’unsu ga ‘yan takarar da suka zaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Majalisar Koli kan Shari’a a Najeriya (SCSN) ta gargadi ’yan siyasa kan duk wani mataki da zai iya haddasa tashin hankali gabanin babban zaben 2027.

Majalisar ta ce babu wani buri ko muradin siyasa da ya cancanci zubar da jinin ’yan Najeriya, inda ta bukaci masu fafutukar siyasa su dauki zabe a matsayin hanyar da kundin tsarin mulki ya tanada domin zabar shugabanni, ba fagen yakar juna ba.

Kara karanta wannan

Abin da ya rage a ƙaddamar da ƴan sandan jihohi a Najeriya duk da ƙorafin ƴan adawa

Sheikh Bashir Aliyu Umar da shugaban INEC
Shugaban kwamitin shari'a, Sheikh Bashir Aliyu Umar da Farfesa Joash Amupitan a dama. Hoto: INEC Nigeria|Bashir Aliyu Umar
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa a cikin sanarwar da sakatarenta, Farfesa Ahmad Bello Dogarawa, ya fitar a ranar Laraba, majalisar ta bukaci ’yan siyasa da magoya bayansu su guji duk wani abu da zai iya haddasa rikici.

Magana kan katin zabe

Majalisar ta bukaci dukkan ’yan Najeriya da suka cancanci kada kuri’a su tabbatar sun mallaki katin zabe na dindindin (PVC), tare da tantance bayanan rajistarsu domin kada su rasa damar shiga zaben.

Rahotanni sun nuna cewa ta kuma bukaci masu zabe su fito su kada kuri’unsu ga ‘yan takarar da suka zaba cikin lumana.

Sheikh Dogarawa ya ce bai kamata bambancin ra’ayin siyasa ya haifar da kiyayya, tashin hankali ko lalata dukiyoyi ba.

An gargadi jam’iyyun siyasa

Majalisar ta bukaci jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu su mayar da hankali kan matsalolin da suka shafi rayuwar al’umma yayin yakin neman zabe.

Ta kuma gargade su da su guji kalaman tunzura jama’a, amfani da bambancin addini da kabila wajen neman goyon baya, barazana da cin mutuncin abokan hamayya.

Kara karanta wannan

Muhimmin tarihi da Tinubu ya kafa game da yaki da ta'addanci a Najeriya

Haka kuma, ta bukaci shugabannin siyasa su hana amfani da ’yan daba, tsoratar da masu zabe da kuma daukar mutanen da za su kawo cikas ga harkokin zabe.

Wajen da ake zabe
Wajen da ake kada kuri'u a Najeriya. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Kiran kwamitin ga jami'an tsaro

Majalisar ta bukaci jami’an tsaro su gudanar da ayyukansu cikin kwarewa da rashin nuna bangaranci, tare da tabbatar da tsaron masu kada kuri’a, jami’an hukumar zabe, masu sa ido da kayayyakin zabe.

Ta yi Allah-wadai da sayen kuri’u, hana mutane kada kuri’a da satar akwatunan zabe, tana mai cewa wadannan ayyuka na tauye wa al’umma damar zabar shugabanninsu cikin ’yanci.

Haka kuma, ta bukaci malaman addinai, sarakunan gargajiya, kungiyoyin fararen hula da kafafen yada labarai su taimaka wajen karfafa zaman lafiya da shiga harkokin zabe cikin lumana.

INEC ta gargadi matasan Najeriya

A wani labarin, mun rahoto cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi kira ga matasan Najeriya da su guji shiga rikicin siyasa gabanin zabe.

Hukumar ta gargadi matasa kan laifuffukan zabe da suka hada da sayen kuri’u, satar akwatunan zabe, tsoratar da masu zabe da kuma lalata kayayyakin zabe.

INEC ta kuma bukaci matasa su rika tantance sahihancin bayanai kafin yada su a kafafen sada zumunta, tare da dogaro da bayanan da hukumomin da abin ya shafa suka tabbatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng