Gwamnatin Najeriya za ta fito da hatsin da aka adana domin karya farashin kayan abinci

Gwamnatin Najeriya za ta fito da hatsin da aka adana domin karya farashin kayan abinci

Gwamnatin Tarayya ta shirya sakin hatsin da ta adana domin kara wadatar abinci da rage tashin farashin kaya a kasuwanni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ministan Noma ya nanata cewa za a kuma raba buhunan takin zamani miliyan uku cikin wata guda domin taimaka wa manoma

Abubakar Kyari ya ce gwamnati na sa ran matakan za su rage kufin noma, kara samar da abinci kuma a daidaita farashin kaya

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin fitar da buhunan hatsin da ta saya ta adana a karkashin shirin Bankin Noma na Najeriya (BOA).

Za a yi wannan ne domin kara yawan kayan abinci a kasuwa da kuma hana hauhawar farashinsu, ana sa ran wannan zai share wa talakawa hawaye.

Abinci
Ministan noma, Abubakar Kyari da buhunan hatsi a jihar Kebbi Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gwamnati ta kuma ce za ta raba buhunan takin zamani miliyan uku cikin wata guda domin rage kudin da manoma ke kashewa a noma a cewar Punch.

Kara karanta wannan

Martanin gwamnatin Kaduna da ADC ta yi zargin ta hana wurin taron siyasa

Ministan Noma da Samar da Abinci, Abubakar Kyari, ne ya bayyana hakan ranar Laraba yayin bikin gabatar da rahoton noman damina a birnin Abuja.

A cewarsa, fitar da hatsin da aka adana na daga cikin matakan da gwamnati ke dauka domin daidaita farashin kayan abinci tare da kare manoma.

Sanata Abubakar Kyari ya ce za a fitar da amfanin gonan da aka saya aka adana karkashin shirin Guaranteed Minimum Price na BOA nan ba da jimawa ba.

Sai dai ministan noman bai bayyana adadin hatsin da za a fitar ko ranar da za a fara rabawa ba.

Ministan ya ce karuwar yawan amfanin gona, fadada filayen noma da saukaka wa manoma wajen samun kayan aikin gona za su hana tashin abinci.

Kyari ya bayyana cewa an samu saukin farashin abinci idan aka kamanta da wancan shekara.

An kuma ji cewa gwamnati da gaske ta ke yi wajen fitar da buhunan taki miliyan uku a wata guda a karkashin Shirin Shugaban Kasa na Takin Zamani.

Mai girma Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya sanar da wannan kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin shugaban ƙasa ya yi wa gwamna Abba Kabir tayin mata

Daily Post ta rahoto Mai girma ministan yana cewa wannan shiri zai taimaka wajen rage kudin noman tare da karfafa wa manoma gwiwar fadada gonakinsu.

Kyari ya kuma yi magana kan Asusun Bunkasa Noma na Kasa da kuma shirin kara jarin Bankin Noma a kokarin da ake yi na inganta rayuwar manoman kasar.

Ya ce shirin Guaranteed Minimum Price yana ba manoma tabbacin kasuwar sayar da amfanin gonarsu, wannan zai taimaka wajen daidaita farashin abinci.

Dangane da bunkasa amfani da injinan noma, Kyari ya ce sun riga ta raba taraktoci 2,000, yayin da ake sa ran fara kawo wasu nan da watanni biyu zuwa uku.

Tsohon sanatan ya kuma bayyana cewa ana samun karuwar masu sha'awar zuba jari a harkar sarrafa amfanin gona, musamman koko, ridi, rogo da goro.

A nan aka ji cewa gwamnati ta rattaba hannu kan yarjejeniyar zuba jarin dala miliyan 33 da wani kamfanin kasar Turkiyya domin wani nau’i na noman zamani.

Abinci
Tarin buhunan abinci a Argungu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng