Tinubu Ya Ba Gawurtaccen Lauya Lambar Yabo ta 2 a Daraja da Mutum Zai Iya Samu

Tinubu Ya Ba Gawurtaccen Lauya Lambar Yabo ta 2 a Daraja da Mutum Zai Iya Samu

  • Mai girma Bola Tinubu ya karrama fitaccen lauya Wole Olanipekun da lambar yabo ta GCON da ake ba wane-da-wane
  • An ba shi lambar yabon ne yayin bikin cikar sa shekaru 75 da haihuwa da kuma shekaru 50 da ya shafe yana aikin lauya
  • Bayan zamansa SAN, Olanipekun ya taɓa shugabantar ƙungiyar lauyoyin Najeriya ta NBA daga shekarar 2002 zuwa 2004

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

FCT, Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya karrama fitacce kuma tsohon lauya Cif Wole Olanipekun SAN, da lambar yabo mai girma.

Wole Olanipekun ya samu Grand Commander of the Order of the Niger wato GCON da ita ce ta biyu mafi girma a jerin lambobin karramawar ƙasar.

Wale Olanipekun
Bola Tinubu da Wale Olanipekun SAN Hoto: @Onanuga1956
Source: Twitter

Bola Tinubu ya karrama Wole Olanipekun da GCON

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis a shafinsa na X (Twitter).

Kara karanta wannan

Fashola ya fito da bayanin da ya kamata mutane su sani kan yanayin lafiyar Tinubu

Bayo Onanuga ya ce Bola Tinubu ya ba Wole Olanipekun lambar yabon ne yayin bikin ƙaddamar da jerin wasu littattafai guda shida da aka wallafa.

An wallafa littatafan ne domin murnar cikar lauyan shekaru 75 da haihuwa, shekaru 50 da soma yin aikin lauya kuma shekara 35 da zamansa SAN.

Onanuga ya bayyana cewa an gudanar da bikin ne domin girmama nasarorin da Olanipekun ya samu a rayuwarsa da kuma fannin shari'a a Najeriya.

Gawurtar Wole Olanipekun wajen aikin lauya

Olanipekun ya zama lauya a Najeriya a shekarar 1976, sannan ya samu matsayin SAN tun a 1991.

Ya taɓa zama shugaban ƙungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) daga shekarar 2002 zuwa 2004, inda ya taka muhimmiyar rawa a harkokin shari'a a ƙasar.

Olanipekun ya ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin fitattun lauyoyin da ake ji da su a ƙasar nan.

Darajar GCON a wajen Gwamnatin Najeriya

Lambar GCON ita ce ta biyu a girma, tana bayan GCFR (Grand Commander of the Order of the Federal Republic) ne kawai da ake ba shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

2027: Sanatan Kano ya faɗawa Tinubu gaskiya kan ƙalubalen da APC za ta fuskanta a Arewa

Yawanci mataimakin shugaban ƙasa, shugabannin majalisar tarayya da alƙalin alƙalai ake ba lambar GCON a al’ada sai kuma wasu da suka yi fice a duniya.

A mulkin Tinubu an bada lambar nan ta GCON ga Gilbert Chagoury da shugabannin Majalisar tarayya, Godswill Akpabio da kuma Tajudden Abbas.

Idan za a tuna, Olanipekun shi ne ya jagoranci tawagar lauyoyin da suka kare nasarar Shugaba Bola Tinubu a APC a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen 2023.

Babban lauyan ya yi galaba a kan lauyoyin Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP a lokacin.

Boyayyiyar matar Goodluck Jonathan

Sai bayan tsawon shekaru aka ji labari ashe mata biyu Goodluck Jonathan yake aure. Dame Patience tana da kishiya, Ayima Lott-Jonathan.

An ji cewa Ayima Lott-Jonathan, amaryarsa za ta kaddamar da littafinta mai suna 'Gold Dust: Treasures of Quiet Years' mai dauke da tarihinta.

Littafin ya ƙunshi tarihin rayuwarta, kuma ta yi bayanin yadda ta ƙoƙarin boye kanta lokacin mulkin mijinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng