Majalisar dokokin jihar Zamfara ta musanta shirin tsige mataimakin gwamna

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta musanta shirin tsige mataimakin gwamna

  • Rikici na ci gaba a tsakanin majalisar dokokin Zamfara da mataimakin gwamnan jihar
  • 'Yan majalisar sun dage cewa mataimakin gwamnan ya bayyana a gabansu don amsa wasu tambayoyi masu muhimmanci
  • Mataimakin gwamnan, a nasa bangaren, yana dogaro ne da umarnin kotu daga Abuja inda ta nemi duk bangarorin da ke cikin rikicin na siyasa da su ci gaba da yadda ake a da

Gusau, jihar Zamfara - Majalisar dokokin Zamfara ta musanta cewa tana shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Mahdi Aliyu Gusau.

Television Continental ta ruwaito cewa ‘yan majalisar sun ce mataimakin gwamnan kawai suke so ya bayyana a gaban majalisar sannnan ya kuma amsa wasu tambayoyi.

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta musanta shirin tsige mataimakin gwamna
Mataimakin gwamna Gusau ya dage kan cewa majalisar ba ta da hurumin tsige shi. Hoto: Mahdi Aliyu Gusau
Asali: UGC

'Yan majalisar suna zargin Gusau da rashin da'a a hukumance da kuma shirya taron siyasa lokacin da jihar ke juyayin mutuwar mutane hamsin da shida da' yan bindiga suka kashe a karamar hukumar Maradun ta jihar.

Mataimakin gwamnan a baya ya yi watsi da gayyatar amma a yanzu ya nuna aniyar amsa gayyatar da zaran umarnin kotu da ya hana majalisar gayyatarsa, ya ba shi damar yin hakan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta nemi a dauki tsatsauran mataki kan masu safarar mutane da sauransu

Jaridar PM News ta ruwaito cewa Gusau yayi tir da shirye-shiryen da ake yi na tsige shi duk da umarnin kotu na dakatar da shirin tsige shi.

Ya ce matakin da majalisar dokokin jihar ta dauka na nuna rashin biyayya ga umarnin kotu kuma hakan zai zama tamkar karya doka ne karara.

Ya lura cewa kotu ta bayar da umarnin kuma Alkalin ya bada umarnin a ci gaba da yadda ake a yanzu, ya kara da cewa 'yan majalisar suna da niyyar ci gaba da shirinsu.

Kotu ta dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara

A gefe guda, wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta bayar da umarnin hana majalisar dokokin jihar Zamfara tsige mataimakin gwamnan jihar, Mahdi Aliyu Gusau.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kotun ta bayar da wannan umarni ne a ranar Litinin, 19 ga watan Yuli, bayan duba karar da Ogwu James Onoja ya shigar a madadin jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan Zamfara ya sa kafar wando daya da ‘yan majalisa, ya ce ba zai gurfana a gabansu ba

A wani bangare na umarnin, Mai shari’a Obiora Egwuatu ya kuma sake gargadi gwamnan jihar Zamfara da babban alkalin jihar kan ci gaba da shari’a dangane da duk wani shirin tsige Mahdi Gusau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng