Hushpuppi: DCP Abba Kyari na fuskantar barazanar kora daga aiki da gurfanarwa, Hukumar ‘yan sanda
- Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta yi magana kan makomar da ka iya samun DCP Abba Kyari idan aka same shi da laifin zargin da ake a kansa
- A cewar hukumar, ana iya korar Kyari, a rage masa matsayi, ko ma a tuhumesa da aikata laifi
- Kakakin hukumar PSC, Austin Braimoh, ya ce hukumar za ta gudanar da bincikenta mai zaman kansa don sanin ko yana da laifi kamar yadda ake ikirari
Akwai yuwuwar idan aka kammala bincike da tabbatar da laifinsa, za a gurfanar da DCP Abba Kyari a gaban kotu sannan a kore shi daga rundunar 'yan sandan Najeriya (NPF).
Kakakin hukumar ‘yan sanda (PSC), Austin Braimoh, wanda ya zanta da Punch a ranar Juma’a, 30 ga watan Yuli, ne ya bayyana hakan a kan binciken da ake yi a zargin alakar Kyari da Abbas Ramon (wanda ake kira Hushpuppi).
Braimoh ya bayyana cewa Kyari na iya fuskantar tuhuma dangane da sakamakon binciken da hukumar ke yi kan manyan zarge-zargen da ake yi masa.
Mai magana da yawun hukumar ya bayyana cewa PSC za ta gudanar da bincike na daban baya ga wanda shugaban ‘yan sanda ya ba da umarnin yi.
Ya bayyana cewa:
"Dokar za ta tantance hukunci daban -daban da za mu iya yanke masa. Za a iya korar shi ya danganta da gwargwadon girman laifin; za mu iya rage masa matsayi, mu rage masa martaba; za mu iya dakatar da shi.
“An gabatar da abubuwa da yawa a gabanmu game da laifuka daban-daban kuma bayan haka, za a mika batun laifin zuwa kotu don gurfanar da shi. Ya danganta da yadda rahoton ke zuwa; ko yana zuwa mana kai tsaye don mu cire ɓangaren masu laifi kuma mu yi maganin shi ko kuma suna so su kula da shi kuma su tura mana wanda yake a hukumance don ladabtar da shi .''
A gefe guda, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Young Progressive Party (YPP), Kingsley Moghalu, ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya mutunta yarjejeniyar mika mutum tsakanin Najeriya da Amurka kan batun da ya shafi mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari.
Kotun Amurka ta nemi FBI ta gabatar da Kyari bisa zarginsa da hannu a zamba na miliyoyin daloli da Hushpuppi da sauran membobin kungiyarsa suka shirya.
Da yake mayar da martani kan lamarin, Moghalu a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, 30 ga watan Yuli, ya ce dole ne a bari dokar kasa da kasa ta yi aikinta yadda ya dace, Channels TV ta ruwaito.
Asali: Legit.ng