2023: Gagarumin nasara yayin da sama da mutum 50,000 suka bar PDP da APGA zuwa APC a jihar Taraba

2023: Gagarumin nasara yayin da sama da mutum 50,000 suka bar PDP da APGA zuwa APC a jihar Taraba

  • Gabannin zaben 2023, jam'iyyar APC ta yi babban kamu a jihar Taraba a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuli
  • Akalla mutane 50,000 ne suka sauya sheka zuwa APC din daga jam'iyyun PDP da All Progressive Grand Alliance (APGA) a jihar
  • Sun sami kyakkyawar tarba daga wani mamba na kwamitin amintattu na jam'iyyar, Dalhatu Sangari

Jalingo, Taraba - Akalla mutane 50,000 a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuli, suka sauya sheka daga jam’iyya mai mulki ta PDP da All Progressive Grand Alliance (APGA) zuwa jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Taraba.

Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa wani mamba na kwamitin amintattu na jam'iyyar, Dalhatu Sangari, wanda ya tarbi masu sauya shekar a Wukari a wani gagarumin biki, ya ce mutanen sun fito ne daga sassa 52 a yankin kudancin jihar.

2023: Gagarumin nasara yayin da sama da mutum 50,000 suka bar PDP da APGA zuwa APC jihar Taraba
APC ta samu sabbin mambobi sama da 50,000 a jihar Taraba Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa Sangari ya lura cewa bikin wani muhimmin ci gaba ne a kokarin jam’iyyar na karbe ragamar shugabanci a jihar saboda hakan bai taba faruwa ba kuma abin mamaki ne.

Kara karanta wannan

Saura awanni 48 ayi zabe, an taso Mai Mala Buni da 'yan kwamitinsa su ajiye shugabancin APC

Ya ce:

“A yau, an bude sabon babi a cikin babbar jam’iyyarmu a nan Taraba. Cikin farin ciki, mun tarbi sama da mutane dubu hamsin akasarinsu daga PDP mai mulki da sauran jam’iyyun siyasa waɗanda suka ga dalilan shiga cikin jam’iyyar saboda gaba.
“Dalilin wannan gagarumin sauya shekar ba boyayye bane. Duk mai hankali zai gaya muku cewa PDP na gab da durkushewa. APC a gefe guda ita ce makoma. Mutanen da ke da hangen nesa ba sa buƙatar a gaya musu hanyar da za su bi. Wannan shine dalilin da ya sa muke samun wannan gagarumin nasara a cikin jam'iyyar a yau."

A cewar rahoton, daya daga cikin wadanda suka sauya shekar Janar Adamu Tubase Ibrahim (Rtd) ya ce ya yanke shawarar komawa APC daga UDP ne saboda yana cikin APC da farko kuma ya bar ta ne kawai saboda rashin adalci.

Kara karanta wannan

Sauya Sheƙa: Wasu Ƴan APC Sun Cinnawa Tsintsiyarsu Wuta, Sun Ce Suna Neman Mafaka a Ƙarƙashin Lemar PDP

Ya ce a matsayinsa na jagoran bangaren marigayiya sanata Aisha Alhassan wacce ta bar APC zuwa UDP, ya ruguje dukkan tsari da zama dan jam’iyya kuma ya shigo da su duka cikin APC don bunkasa damar da jam'iyyar ke da shi wajen cimma burinta a 2023 da gaba.

Fani Kayode, Shehu Sani sun ziyarci gwamnan da ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, ana rade-radin za su bi sahu

A gefe guda, Femi Fani-Kayode, jigo a jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), ya ziyarci gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara a Abuja.

Jigon na PDP ya bayyana hakan ne ta wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a, 30 ga watan Yuli.

Legit.ng ta lura cewa hotunan da tsohon ministan sufurin jirgin ya wallafa sun kuma nuna cewa Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna, shima yana tare da Gwamna Matawalle.

Kara karanta wannan

2023: Shugabannin APC na so Gwamna Lalong ya gaji Shugaba Buhari

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel